AFIRKA
5 minti karatu
Hanyoyin ruwa masu hatsari: Dalilan da ke sa Nijeriya fuskantar hadurran jiragen ruwa a-kai-a-kai
Hatsarin jirgin ruwa na baya bayan nan da ya afku a Nijeriya ya yi ajalin akalla mutane 60, wanda hakan ke karin haske kan yadda kogunan kasar suka zama masu hatsari saboda rashin kulawa, inda ake take dokokin kariya da rashin kayan tsira.
Hanyoyin ruwa masu hatsari: Dalilan da ke sa Nijeriya fuskantar hadurran jiragen ruwa a-kai-a-kai
Hatsarin jiragen ruwa a Nijeriya lokacin damina ya zama ruwan dare. / Reuters
17 awanni baya

Kututturen bishiya na nan kafe a bakin kogin, wa ya san tsawon lokacin da yake a wajen, itacen da ba a iya gani da ke ƙarƙashin ruwan Kogin Neja.

Wata tsawa da aka yi ta wargaza nutsuwar wajen, tare da saka fasinja masu yawa yin kururuwa a cikin jirgin ruwan katako. Babu makawa kwale-kwalen ya gamu da jarrabar nutsewa.

Yayin da ake ta kukan neman agaji, masu aikin ceto daga kauyuka makota da ke kusa da su sun kunna nutso don ceton duk wanda suka iya gani na yawo a saman ruwa. Ga wasu da dama, taimakon ya zo a makare.

Mahukunta sun ce jirgin ruwan, da ke dauke da mutane sama da 100 da ke hanyar zuwa gaisuwar ta’aziyya, ya nutse ne a kusa da kauyen Gausawa da ke Borgu a jihar Neja ta arewa ta tsakiyar Najeriya.

Akalla rayuka 60 aka rasa sakamakon hatsarin da ya faru a ranar 2 ga Satumba, wanda ya afku a yanayin da aka saba gani a kasar.

Karya ka’idoji karara

Manyan matattarar ruwa a Najeriya - masu tsawon kilomita 8,600 wanda suka zama koguna na uku mafi tsawo a Afirka bayan Chadi da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo - na zama kadarorin tattalin arziki kamar yadda suke abubuwan al'ajabi.

Wadannan hanyoyi, da suka taso daga kogunan Neja da Benue zuwa iyakar gabar teku daga Badagry zuwa Calabar, suna hada al’ummomin karkara da kuma zama hanyoyin sufuri na harkokin noma.

Abin da ake gani koyaushe shi ne ibtila’i, kamar yadda ya faru a Gausawa a wannan makon, shi ne yadda masu tuka wa da kula da kwale-kwalen ke ci gaba da kin bin ka’idojin tuki a kan hanyoyin ruwa.

Wani bincike da aka buga a cikin wata mujallar kasa da kasa da ake kira ‘International Journal of Scientific Research’ ya bayyana cewa tsakanin shekarar 2010 zuwa karshen 2021, an yi asarar rayuka 2,346 sakamakon hadurran jiragen kwale-kwale 266.

Shekara mafi muni da aka shaida ita ce 2021. Fiye da kashi 67% na waɗannan hadurra an bayyana za a iya hana su afku wa, kuma kuskure ko gangancin mutane ne suka janyo su - lodin da ya wuce ka’ida, rashin gyara da take dokokin tsaro.

Bayanan da aka samu tare da Hukumar Kula da Koguna ta Najeriya ta tabbatar da sakamakon binciken.

“akwai dokokin da suka shafi koguna da hanyoyin ruwa, amma abin takaici, ba a aiki da su,” in ji Ibrahim Hussaini, daraktan yada labarai da ayyuka na musamman a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, yayin zanta wa da TRT Afrika.

Yawan zirga-zirgar ababen hawa a goguna da gabar teku, ciki har da jiragen ruwa manya da ke dauke da tan tan na kayan abinci, na kawo hatsarin karon jirage ko a yi karo da wani abu marar kyau.

A shekarar 2018, fasinjoji goma sha daya ne suka mutu a Legas, yayin da wani jirgin ruwa ya daki wani jirgin ruwan katako a kusa da gabar ruwan Apapa.

Abbas Garba Idriss, shugaban Kungiyar Masu Inshorar Hasurra ta Najeriya, ya bayar da shawarar horaswa ta musamman ga matukan jiragen ruwa da ke zirga-zirga a kan hanyoyin da ke cike da zirga-zirgar jirage.

Ya kuma bayar da shawarar saka ka’idoji masu tsauri ga kowanne direba kafin ya fara tuka jirgin ruwa.

"Ya kamata su iya karanta kayan aikin da ke faɗakar da su game da tunkarar jiragen ruwa, matsaloli da ma rashin kyawun yanayi," Idriss ya shaida wa TRT Afrika.

Hanyoyi da ke cike da tarnaki

Bayan kuskuren ɗan adam, kogunan na Najeriya sun ƙara zama cikin hatsari saboda rashin kulawa. Masanin harkokin tsaro Moses Ochonogor ya yi imanin cewa kula da manyan hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa na iya kawar da afkuwar hadurra da dama.

“Ya kamata a rika duba hanyar kogi ta jihar Neja da hatsarin ya afku a ranar Talatar da ta gabata, da a ce an sa ido sosai, da an yi gargadi kan kututturen bishiyoyin da ke nutse a cikin ruwa, da kuma aike wa masu aikin jirgin ruwa sakon gargadi.” Inji shi.

Babban gibin da ke tattare da kayan ayyukan ceto a kasar na kara yiwuwar samun asarar rayuka a duk lokacin da wani hatsari ya faru.

"Babu wani jirgin ruwa da ya kamata yahau ruwa ba tare da muhimman kayan ceto da kariya ba.

“Wannan ya kamata ya zama mafi ƙarancin ma'auni. Samun masu taimako da suka samu horo a cikin jirgin na iya zama shinge tsakanin rayuwa da mutuwa," in ji Idriss.

Adadin mutanen na kara yawa a kowanne lokacin damina inda kanun labarai ke fitar da bayanan jiragen ruwan da suka nutse da mutane a koguna.

A watan Disambar shekarar da ya gabata, mutane 54 ne suka nutse a kogin Neja bayan da wani kwale-kwalen da ya lodi mutanen da suka wuce kima inda ya dau fasinjoji sama da 200 ya nutse.

Yunkurin tabbatar da aiki da doka

Alhamdulillahi, hukumomi sun fara amince wa da matsalar tsaro da ke addabar koguna da hanyoyin ruwa a Najeriya.

Hussaini ya ce hukumarsa ta kara kaimi wajen gangamin samun kariya a kan ruwa a yankunan karkara inda aka kuma samar da hukunci mai tsanani ga duk wanda ya saba ka’idojin.

"Muna so mu tabbatar da cewa karya dokokin ya zama mai wahalai aikata wa sosai," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Tare da dogaron da Najeriya ke da shi kan bunkasar hanyoyin ruwanta, kwararru sun bayar da shawarar zuba jari mai girma a fannin sa ido, aiwatarwa da wayar da kan jama'a don rage afkuwar hadurran.

"Tsarin sufurin ruwa ya kamata ya zama kadara ga Najeriya," in ji Idriss. "Amma har sai an bayar da fifiko kan tsaro da bin dokoki, dan ba haka ba, to za mu ci gaba da fuskantar ibtila’o’i.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us