A kowace shekara, lokacin da ruwan sama mai yawa ya fara sauka a kasashen Kudancin Afirka, wani canji mai ban mamaki na faruwa a cikin dazuzzukan mopane na Namibia.
Daga ganyen bishiyar mopane, wani abinci mai daraja na kakar yana bayyana: tsutsar mopane, wata tsutsa da ake daraja ta sosai tsawon shekaru a tsakanin al’umar Ovambo da Caprivian a arewa ta tsakiyar Namibia.
Ga baki, waɗannan ƙananan halittu masu tsawon inci ɗaya na iya zama kamar ba su dace da zama abinci ba. Amma a wajen wasu Namibiyawa, zuwan tsutsar mopane—wadda ake kira ombidi a yaren gida—yana nufin abubuwa sama da abinci. Yana nuna lokacin girbi ya yi, aiki tare, da haɗin kai da kakanni.
Mata da yara na taruwa a cikin daji, suna tattara tsutsotsin da hannu kafin a tsabtace su, a tafasa su a cikin ruwan gishiri, sannan a shimfiɗa su a ƙarƙashin rana don su bushe.
A al'ada, ana haɗa su cikin miya da tuwo. Omagungu da Nshimu (tsutsar mopane da tuwon masara) sun kasance shahararrun abinci da mutanen yankin ke ci.
Amma kamar yadda tsutsar ke canzawa zuwa babbar tsuntsuwa mai suna emperor moth, tsutsar mopane ba kawai abincin gargajiya ne da aka keɓe wa kabilun Namibiya da suka wanzu tsawon karni da dama ba.
Gidajen cin abinci na zamani suna gwada yin sabbin girke-girke da tsutsar.
Masu dafa abinci suna amfani da bidiyoyin Instagram da TikTok don nuna tsutsar da aka soya tare da tafarnuwa da barkono sannan a tsoma su cikin miya ko kuma a yi amfani da su a matsayin kayan ado mai ƙyalli a kan salatin zamani.
Masu dafa abinci na Kudancin Afirka, kamar Adriano Visagie da Ritshidze Sibadali, suna ganin waɗannan girke-girken a matsayin alamar alfahari da abincin gargajiya na gida.
“Za a iya cin tsutsar mopane a bushe a matsayin abin ci na ‘crispy’ ko kuma a soya su da gishiri kaɗan,” in ji Adriano Visagie a cikin ɗaya daga cikin bidiyonsa na TikTok.
Ga wasu a cikin ƙasar, tsutsar mopane ma tana zama hanyar samun kuɗi. A wasu sassan Zambezi da Kavango, iyalai na samun kuɗin shiga ta hanyar sayar da tsutsotsin da aka busar a kasuwanni ko gefen hanya, inda sau da yawa suke samun farashin da ya ta fi na nama tsada.
A 'yan kwanakin nan, girbin tsutsar mopane ya ɗauki sabon salo na kasuwanci.
Tsutsotsin mopane da ake samarw, yawanci ana sanya su a cikin gwangwani tare da miyar tumatir, miya mai barkono, ko kuma ruwan gishiri, kuma ana samun su a kasuwannin karkara a fadin Kudancin Afirka.