AFIRKA
3 minti karatu
Kwamitin Sulhu na MDD ya yi watsi da yunƙurin RSF na kafa sabuwar gwamnati a Sudan
Majalisar ta nemi a tsagaita wuta cikin gaggawa a El Fasher, tana mai cewa wani yunƙuri da dakarun RSF ke yi na kafa sabuwar gwamnati zai ƙara rura wutar rikici a Sudan.
Kwamitin Sulhu na MDD ya yi watsi da yunƙurin RSF na kafa sabuwar gwamnati a Sudan
Sojojin Sudan na tafiya kusa da motocin da aka kona bayan wata fafatawa da suka yi da dakarun RSF a Khartoum babban birnin kasar Sudan. / Reuters
14 Agusta 2025

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi watsi da sanarwar da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka yi na kafa sabuwar gwamnatin hamayya a Sudan, yana mai gargaɗin cewa hakan na barazana ga haɗin kan ƙasar da daidaiton yankuna da kuma zaman lafiyar yankin.

"Mambobin kwamitin sulhun sun yi watsi da sanarwar kafa wata gwamnati a yankunan da dakarun RSF ke riƙe da iko da su," kamar yadda majalisar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, tana mai nuna “damuwa” kan cewa matakin na iya wargaza ƙasar da kuma ta'azzara matsalar jinƙai.

Kazalika ta jadadda "ƙudurinta na tabbatar da 'yancin kai da cin gashin kai da kuma haɗin kai a ƙasar Sudan, tana mai jaddada cewa matakin na barazana ga makomar Sudan da zaman lafiya a yankin baki ɗaya.

Mambobin kwamitin sun bayar da misali da ƙuduri mai lamba 2736 da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da shi a watan Yuni, wanda ya buƙaci dakarun RSF su janye daga mamayar da suka yi wa El Fasher - hedkwatar Jihar Darfur ta Arewa kana wata babbar cibiyar jinƙai - tare da dakatar da hare-hare a yankunan da ke kewaye da inda aka samu rahoton aukuwar yunwa da matsanancin ƙarancin abinci.

"Mambobin Ƙwamitin Sulhun sun buƙaci RSF ta ba da damar kai agajin jinƙai zuwa EL Fasher,’’ in ji sanarwar, tana nuni kan rahotanni kai sabbin hare-haren RSF a birnin.

Ofishin kare hakkin bil adama na MDD ya ce bayanan farko sun nuna cewa aƙalla fararen-hula 57 ne suka mutu a wani hari da dakarun RSF suka kai a ranar Linitin, ciki har da mutane 40 da suka rasa matsugunansu a sansanin Abu Shouk.

Majalisar ta kuma yi Allah wadai da hare-haren baya bayan nan a yankin Kordofan na ƙasar Sudan, inda ta ce sun yi sanadin salwantar da rayukan fararen-hula tare da daƙile ayyukan jinƙai.

Ƙira don tattaunawa

Mambobin majalisar sun jaddada cewa, sake tattaunawa na da matuƙar muhimmanci don dakatar da yaƙin, da kuma samar hanyoyin tsagaita wuta mai ɗorewa wanda hakan zai share fagen sasanta rikicin siyasa wanda ya haɗa dukkan masu ruwa da tsaki na siyasa da zamantakewar Sudan.

Sun buƙaci dukkanin ɓangarorin da su kare fararen-hula, da kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa da kuma bin ƙuduri mai lamba 2736, tare da yin kira da a ɗauki alhakin aikata manyan laifuka.

Sanarwar ta kuma buƙaci dukkan jihohin ƙasar su guji ayyukan da za su iya rura wutar rikici tare da tallafa wa ƙoƙarin samar da ɗorewar zaman lafiya.

A halin yanzu dai RSF na riƙe da sassan Arewa da Yammacin Kordofan, da kuma Kordofan ta Kudu da Blue Nile, sai yankuna huɗu na jihohi biyar na Darfur.

Rikici tsakanin sojojin Sudan da RSF ya ɓarke ne tun a watan Afrilun 2023, inda ya kashe mutane fiye da 20,000 tare da raba fiye da miliyan 14 da matsugunansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Kazalika, bincike daga wata Jami'ar Amurka ya ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 130,000.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us