Babban Bankin Ƙasar Ghana (BoG) ya fitar da sabon umarni wanda ke buƙatar masu shigar da kayayyaki da ke amfani da kuɗaɗen ƙetare su tabbatar cewa sun ba da bayanan da ake buƙata a rubuce, a wani ɓangare na matakan hana halatta kuɗin haram.
Umarnin, wanda Misis Aimee V. Quashie ta sanya wa hannu a madadin sakataren bankin, ya gyara ƙa’idojin shiga da fitar da kuɗaɗen ƙetare, kamar yadda kamfanin dillancin ƙasar Ghana ya rawaito.
Wani muhimmin ɓangare na gyaran ya mayar da hankali kan masu shigar da kayayyaki cikin ƙasar, waɗanda a yanzu ya zama dole su samar da wasu takardu domin amfani da kuɗaɗen ƙetare wajen ciniki a harkar kasuwancinsu.
Sanarwar ta BoG ta ce ana buƙatar masu shigar da kayayyaki ƙasar su gabatar da:” takardar shaidar ofishin kuɗin ƙetare da shaidar banki a matsayin hujjar cire kuɗin a banki ko kuma siyansa, da kuma takardar shiga da kaya da aka sanya wa hannu da rasiti da kuma kwantiragi.”
An ɗauki wannan matakin ne domin a tabbatar da bin gaskiya da kuma halascin cinikayya ta ƙetare.
Kazalika, matakin na nufin hana wanzuwar kuɗin haram ta hanyar samar da takardun da za a iya bibiya kan duk wata muhimmiyar cinikayya da masu shigar da kayayyakin ƙasar suka yi.
Sanarwar ta jaddada cewa ƙin bayyana kuɗaɗe da yin bayani na ƙarya ko kuma gaza gabatar da takardun da ake buƙata zai sa a ƙwace kuɗaɗen da ba a bayyana ba nan take, ko ƙaƙaba tara ko kuma gurfanarwa a gaban kotu.