GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Ƙasashen Afirka sun yi Allah wadai da yadda Isra’ila ta keta alfarmar 'yancin kan Qatar
Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUC) ya yi gargaɗin cewa harin na iya barazana ga yanayi mai raunin da ake ciki a gabas Ta Tsakiya.
Ƙasashen Afirka sun yi Allah wadai da yadda Isra’ila ta keta alfarmar 'yancin kan Qatar
Wani gini da ya lalace, bayan wani harin Isra’ila kan shugabannin Hamas, a cewar wani jami’in Isra’ila a Doha, Qatar / REUTERS
13 awanni baya

Ƙasashen Afirka da Ƙungiyar Tarayyar Afrika sun yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ta kai ranar Talata kan shugabannin Hamas a Qatar, suna masu gargaɗin cewa ta keta ‘yancin kan ƙasar.

Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AUC) ya yi gargaɗin cewa harin zai iya barazana ga yanayi mai rauni da ake ciki a Gabas Ta Tsakiya.

Mahmoud Ali Youssouf ya yi nuni da rawar da Qatar ke takawa a wajen shiga tsakani na diflomasiyya yana mai kira da “a sabunta tattaunawa domin samun zaman lafiya na adalci mai ɗorewa a Gabas Ta Tsakiya”.

Ministan Harkokin Wajen Masar ma ya bayyana harin na Isra’ila a matsayin “tsabar keta dokar ƙasa da ƙasa da kuma ‘yancin kan ƙasa.”

‘Misali mai haɗari’

Masar ta ce harin ya kasance “wani misali mai haɗari kuma wata taɓarɓarewa da bai kamata a lamunta ba.”

Ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Qatar kuma ta buƙaci ƙasashen duniya su ɗauki mataki nan take kuma su hukunta Isra’ila.

Somaliya ta ce hare-haren Isra’ila daidai yake da “keta dokokin ƙasa da ƙasa” kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro na yankin da ma duniya baki ɗaya.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us