GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Isra'ila ta kai hari kan shugabannin Hamas da suka taru a Qatar don tattaunawa kan tsagaita wuta
Qatar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira harin matsorata da Isra'ila ta kai kan kasarta.
Isra'ila ta kai hari kan shugabannin Hamas da suka taru a Qatar don tattaunawa kan tsagaita wuta
An ga hayaƙi na tashi bayan da aka ji ƙarar fashewar wani abu a Doha. / Reuters
9 Satumba 2025

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kai wani hari kan manyan shugabannin kungiyar Hamas, ko da yake ba ta bayyana inda aka kai harin ba.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da kafafen yada labarai daga Qatar suka ce an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Doha babban birnin kasar, tare da turnuƙin hayaƙi da ke tashi sama.

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Isra'ila ya shaida wa kafofin yada labaran kasar cewa harin ya rutsa da mataimakin shugaban kungiyar Hamas Khalil al-Hayya da kuma babban jami'in kasar Zaher Jabareen.

Wata tawagar shugabannin Hamas ta tsallake rijiya da baya a harin na Doha, kamar yadda wani babban shugaban kungiyar ya shaida wa Al Jazeera.

Jami’an Isra’ila sun kuma shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an kai harin ne kan shugabannin Hamas a Qatar, sai dai ba a sami karin bayani kan asarar rayuka ko kuma girman harin ba.

Tashar talabijin ta Aljazeera, ta nakalto majiyar kungiyar Hamas, ta rawaito cewa an kai hari kan tawagar sasantawar kungiyar a wani taro a birnin Doha inda suke tattaunawa kan ƙudirin tsagaita wuta na baya bayan nan na shugaban Amurka Donald Trump.

Qatar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira harin matsorata da Isra'ila ta kai kan ƙasarta, tana mai cewa harin na nuni da "keta dukkan dokokin ƙasa da ƙasa".

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin "a mataki mafi girma".

A halin da ake ciki, tashar Channel 12 ta Isra'ila ta ambato wani jami'in Isra'ila yana mai cewa Trump ya ba da "izinin" kai farmakin da aka kai wa shugabancin Hamas a Qatar. Jami'in ya kara da cewa an sanar da Washington kafin kai harin.

An kashe ɗan shugaban Hamas Khalil al-Hayya da daraktan ofishinsa a harin da Isra'ila ta kai a Doha, in ji babban jami'in kungiyar Suhail al-Hindi kamar yadda ya shaida wa Al Jazeera.

Kazalika jami'an Hamas sun shaida wa TRT cewa tawagar Hamas ta sasancincin ta tsira daga harin, amma an kashe wasu masu rakiya da masu tsaron lafiya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us