Kungiyar Agaji ta Red Cross ta ce hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaza, da nufin mamaye birnin a yankin Falasdinawa da aka yi wa ƙawanya abu ne da ba za a iya jurewa ba.
Babban mai magana da yawun Ƙungiyar Agaji ta Red Cross Christian Cardon ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, tsananin tashin hankali a Gaza na nufin ƙarin kashe-kashe, da rasa matsugunai, da ɓarna da kuma jawo firgici.
"Gaza wani rufaffen waje ne, wanda babu wanda zai iya tserewa daga gare shi, kuma inda babu hanyoyin samun lafiya da abinci da tsaftataccen ruwan sha," in ji Cardon.
Isra'ila ta yi luguden wuta kan birnin Gaza da wajensa a cikin dare, kamar yadda mazauna garin suka fada a ranar Alhamis, yayin da sojoji suka sanar da daukar matakin farko a yunkurinsu na ƙwace babbar tunga ta karshe ta kungiyar Hamas.
Sabon shirin da aka amince da shi ya ba da izinin yin kira ga kusan sojojin ko-ta-kwana 60,000, tare da zurfafa fargabar kamfen din zai kara dagula rikicin jinƙai da ya riga ya yi a Zirin Gaza.
"Ba jira muke ba, mun fara matakin farko, kuma a yanzu haka, sojojin IDF na riƙe da wajen Birnin Gaza," in ji rundunar sojin Isra'ila.
Mazauna Birnin Gaza sun bayyana yadda suke shan hare-haren bama-bamai a cikin dare.
"Gidajenmu suna girgiza duk tsawon dare - ga ƙarar fashewar bama-bamai da harbe-harben manyan bindigogi da ƙarar jiragen yaƙi da na motocin daukar marasa lafiya, da kukan neman agaji duk suna figita mu da neman kashe mu," a cewar daya daga cikin mazauna garin ga AFP.