Wasu ma'aikatan kamfanin dillancin labarai na Reuters da ke ƙasar Birtaniya, sun yi bayani a cikin wani rahoto da aka fitar a ranar Alhamis game da abin da suka kira son kai da nuna goyon baya ga Isra'ila daga ɓangaren editoci da shugabannin kamfanin.
A farkon wannan watan, bayan Isra'ila ta kashe ɗan jaridar Falasdinawa Anas Al Sharif, Reuters ta wallafa wani labari mai taken, "Isra'ila ta kashe dan jaridar Al Jazeera da ta ce shi jagoran Hamas ne." Wannan zabi na taken ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman ganin cewa Al Sharif ya taɓa kasancewa cikin tawagar Reuters da ta lashe lambar yabo ta Pulitzer a shekarar 2024, kamar yadda Declassified UK ta ruwaito.
Taken labarin ya haifar da martani mai zafi a shafukan intanet tare ƙara samun da damuwa a tsakanin ma'aikatan Reuters, inda wasu daga cikinsu suka bayyana damuwarsu a sirrance game da abin da suka kira nuna goyon baya a ra’ayin editocin kamfanin.
Reuters, wanda aka kafa a birnin London a shekarar 1851 kuma yanzu yana isa ga mutum fiye da biliyan ɗaya a kullum, yana fuskantar ƙarin bincike daga cikin gida.
Wasu ma'aikatan yanzu da na baya na Reuters, waɗanda suka yi magana a sirrance da Declassified UK, sun bayyana al'adar wata al’ada da editocin kamfanin suke da ita na rashin bayar da muhimmanci ga labarin Falasɗinawa.
Wani edita ya yi murabus a watan Agustan 2024, ya ce ya yi murabus ɗin ne sakamakon ɗabi’un kamfanin ba su dace da yadda suke bayar da rahoto a kan yaƙin da Isra’ila ke yi da Gaza ba.
Editan ya hada da rahoto da wata wasika a bude, yana kira ga shugabannin su bi ka'idojin aikin jarida; duk da haka, sashen sadarwa na Reuters ya musanta samun su.
Duk da haka, wasu daga cikin gida sun tabbatar wa Declassified UK cewa bayan yakin Isra'ila da Gaza, wata tawagar 'yan jarida ta Reuters ta gudanar da bincike na cikin gida kan kusan labarai 500 da suka shafi Isra'ila da Falasdinu da aka wallafa cikin makonni biyar.
Binciken ya nuna son kai mai yawa, inda aka fi karkata hankali ga ɓangaren Isra'ila da asarar rayukan da suka yi, duk da cewa adadin mutanen da suka mutu a Gaza ya ninka na Isra'ila sau goma.
A lokacin, fiye da Falasdinawa 11,000 ne suka mutu. Wata majiyar Reuters ta shaida wa Declassified UK cewa: "Bayan makonni kadan da yakin Isra'ila da Gaza, wasu 'yan jarida a Reuters sun gane cewa rahotanninmu game da yakin Isra'ila da Gaza ba su da adalci."
Rahoton cikin gida na 'yan jaridar ya kuma soki Reuters saboda kin amfani da kalmar "Falasdinu" da kuma rashin rufe ikirarin masana cewa Isra'ila tana aikata kisan kare dangi, kamar yadda Reuters take bayyanawa a fili ga yaƙin Rasha da Ukraine.