AFIRKA
2 minti karatu
An katse wutar lantarki a Sudan yayin da dakarun sa-kai ke kai hare-haren jirage sama: Rahoto
Jiragen sama marasa matuƙa sun kai hari a yankin soja na Wadi Seidna da tashar wutar lantarki ta Al-Markhiyat a birnin Omdurman, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.
An katse wutar lantarki a Sudan yayin da dakarun sa-kai ke kai hare-haren jirage sama: Rahoto
Harin ya haddasa katsewar wutar lantarki a faɗin birnin, kamar yadda shaidu suka tabbata / Others
19 awanni baya

Hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka kai sun shafi wurare daban-daban a jihar Khartoum ta Sudan, wanda ya haddasa babbar katsewar wutar lantarki, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito a ranar Talata.

Jaridar Sudan Tribune ta ambaton shaidu tana cewa jiragen sama marasa matuƙa sun kai hari a yankin soji na Wadi Seidna da kuma tashar wutar lantarki ta Al-Markhiyat da ke birnin Omdurman.

Harin ya haddasa katsewar wutar lantarki a faɗin birnin, kamar yadda shaidu suka tabbatar.

Bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna yadda taransufoma ta lantarki a tashar ta kama da wuta bayan jerin fashe-fashe.

Dakarun RSF sun kuma kai hari a unguwar Al-Kalakla ta Khartoum, inda wata masana'antar soji take, kamar yadda Sudan Tribune ta ruwaito.

Har ila yau, an kai hari a garin Al-Jaili, wanda ke dauke da babbar matatar mai ta kasar, kamar yadda aka bayyana.

Ba a samu rahoton asarar rayuka ba.

Harin ya biyo bayan kwanaki kadan da sojojin Sudan suka ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan soji a Kordofan, tsakiyar Sudan, domin sake karbe iko da manyan birane a yankin da kuma karya takunkumin RSF a birnin Al Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa.

Tun daga watan Mayun 2024, Al Fasher ta sha fama da rikici mai tsanani tsakanin sojojin Sudan da RSF, duk da gargadin ƙasashen duniya kan haɗarin tashin hankali a birnin da ke zama cibiyar agaji ga jihohin Darfur guda biyar.

RSF da sojojin kasar sun kasance cikin rikici mai tsanani na neman iko tun watan Afrilun 2023, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da jefa Sudan cikin daya daga cikin mafi munin matsalolin jinƙai a duniya.

Fiye da mutum 20,000 sun mutu kuma mutane miliyan 15 sun rasa matsugunansu, kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya da na cikin gida suka nuna.

Sai dai, masu bincike daga Amurka sun ƙiyasta cewa adadin mutanen da suka mutu na iya kaiwa har 130,000.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us