AFIRKA
2 minti karatu
Kamfanin lantarkin Ghana na son ƙara kuɗin wuta da kashi 225 cikin 100
Kamfanin makamashin ya ce wannan babban ƙarin ya zama tilas ne domin kauce wa durƙushewar harkar makamashin da kuma tabbatar da samar da wutan da za a iya dogaro a kai.
Kamfanin lantarkin Ghana na son ƙara kuɗin wuta da kashi 225 cikin 100
Sai hukumar PURC ta amince da ƙarin kuɗin dagon wutar kafin a aiwatar da shi. / Picha: Reuters
9 Satumba 2025

Rahotanni daga Ghana na cewa kafamin wutar lantarki na ƙasar (ECG) ya gabatar da shawarwari na ƙara kuɗin dakon wuta da kashi 225 cikin 100 ga hukumar da ke sa ido kan ababen amfanin yau da kullum (PURC).

Kamfanin makamashin ya ce wannan babban ƙarin ya zama tilas ne domin kauce wa durƙushewar harkar makamashin da kuma tabbatar da samar da wutar da za a iya dogaro a kai.

Sabon kuɗin dakon wutar da ake son a yi amfani da shi zai tayar da kuɗin dakon wuta daga Cedi na Ghana 19.0384 ga ko wane kilowatt a ko wace sa’a zuwa cedi 61.8028 ga ko wane kilowatt a ko wace sa’a tsakanin shekarar 2025 zuwa 2029.

Kamfanin, wanda ke bai wa kashi 73 cikin 100 na ‘yan Ghana wuta da kuma ba da wuta ga mutum miliyan 4.87, ya ce kuɗin da ake biya na yanzu ba zai iya ɗorewa ba.

Kamfanin wuta na ECG ya ce kuɗin dakon wuta ya ƙunshi kashi 11 cikin 100 na kuɗin harkar lantarki, ƙasa da yawan kason kuɗin a ƙasashen duniya inda ya kai kashi 30 zuwa 33 cikin 100.

Giɓin da kuma faɗuwar darajar kuɗin cedi na Ghana wanda ya rasa kashi 74 cikin 100 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, ya jawo raguwar darajar kuɗin shigar kamfanin da kashi 45 cikin 100.

Domin magance waɗannan matsalolin da kuma  ƙorafe-ƙarafen mutane game da ingancin aikin kamfanin, kamfanin wutar Ghana ECG ya gabatar wani cikakken shiri na saka sabon kuɗin shigar cikin muhimman kayayyakin aiki.

Kamfanin makamashin ya bayyana cewa ya riga ya kashe dalar Amurka miliyan 408 tun shekarar 2022 kan sabbin ƙananan tashoshi da injuna masu aiki da kansu da kuma mita ta zamani har miliyan ɗaya.

Za a yi amfani da sabon kuɗin dakon ne ta wajen ci-gaba da waɗannan ayyukan domin inganta samar da wuta.

Kamfanin ya ce sabon kudin dakon zai taimaka masa wajen rage yawan ɗauke wuta.

Kawo yanzu dai ba za a aiwatar da wannan ƙarin ba har sai lokacin da hukumar PURC mai sa ido kan ababen amfanin yau da kullum ta amince da shi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us