Falasɗinawa a Gaza da aka yi wa ƙawanya sun gudanar da jana'iza a farfajiyar asibitin Nasser ga 'yan jaridar da Isra'ila ta kashe a harin da ta kai asibitin Khan Younis da ke kudancin Gaza.
'Yan jaridar da Isra'ila ta kashe sun haɗa da Hussam Al Masri, wanda ya yi aiki a matsayin ɗan jarida mai ɗaukar hoto na kamfanin dillancin labarai na Reuters; Mariam Abu Daqqa, 'yar jaridar wasu kafafen yaɗa labarai, da suka haɗa da The Independent Arabic da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press; Ahmed Abu Aziz, wanda ya yi aiki da Quds Feed Network, da Mohammed Salama na Al Jazeera da kuma mai ba da gudunmawa ga kamfanin dillancin labarai na Reuters Moaz Abu Taha.
Harin ya kashe Falasɗinawa aƙalla 20, ciki har da 'yan jaridar, a cewar hukumomin Gaza.
A wani harin na daban sojojin Isra'ila sun harbe wani ɗan jarida Bafalasɗine Hassan Douhan a Khan Younis.
Kisan gillar da aka yi wa ‘yan jaridar ya sanya adadin ‘yan jaridar da aka kashe a Gaza tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 246.
Ga wasu hotuna masu ratsa zuciya: