Harin sama na Isra’ila kan cibiyar lafiya ta Nasser Medical Complex a Khan Younis ya kashe ‘yan jarida biyar ranar Litinin.
Daga cikinsu akwai mai ɗaukar hoto Moaz Abu Taha da Mariam Abu Daqqa da mai ɗaukar bidiyon gidan talabijin na Palestine TV Hussam al-Masri, da kuma ɗan jaridar Al Jazeera Mohammad Salama da ma’aikacin kwantaragi na Reuters Hatem Khaled, in ji majiyoyin lafiya da kuma kafar watsa labaran da ke Qatar.
Kashe-kashe na baya bayan nan sun nuna irin gagarumar ta’adin da yaƙin ya yi a kan ‘yan jaridan Gaza, lamarin da ya mayar da yankin wuri mafi hatsari ga ‘yan jarida a duniya.
Daga farko a cikin ƙarshen mako, ƙungiyar ‘yan jarida ta Falasɗinu ta tabbatar da cewa harsasan Isra’ila sun harbe Khaled al-Madhoun, wani maiɗaukar bidiyo wa kafar Palestine TV, a yankin Zikim da ke yankin arewacin Gaza yayin da yake ɗaukar bidiyon fararen hula da ke neman taimakon jinƙai.
Kashe kashen sun biyo bayan wani hari na ranar 10 ga watan Agusta a birnin Gaza inda aka kashe ‘yan jaridan Al Jazeera shida.
Hukumomin Isra’ila daga bisani sun zargi ɗaya daga cikin ‘yan jaridan da aka kashe cewa kwamandan Hamas ne ba tare da gabatar da hujja ba.
Tun lokacin da yaƙin na Isra’ila ya fara ranar 7 ga watan Okotoban shekarar, 2023, aƙalla ‘yan jarida da ma’aikatan kafafen watsa labarai 244 ne hare-haren Isra’ila suka kashe, bisa ga ƙididdigar TRT World.
Sama da ‘yan jarida 500 da ma’aikatan kafafen watsa labarai ne suka raunata ko rasa gidajensu ko kuma aka tilasta musu zama ‘yan gudun hijira.
Isra’ila ta musanta kai hare-hare da gangan kan manema labarai, amma ƙungiyoyi masu sa ido ciki har da Reporters Without Borders (RSF) da kuma ƙungiyar ‘yan jarida ta duniya (IFJ) sun yi Allah wadai da abin da suka kira "hare haren kan ‘yan jarida da ba a taɓa gani ba" kuma sun nemi a yi bincike na ƙasa da ƙasa mai cin gashin kansa kan lamarin.