GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Isra'ila ta rusa duka unguwar Al Zeitoun mai gidaje fiye da 1,500 a Birnin Gaza
A yayin da Israila ke zafafa hare-harenta ta ƙasa, an yi amfani da manyan makamai da bama-bamai wajen rusa Kudancin Al Zeitoun da mayar da ita kufai, tare da korar mazauna yankin lamarin da ya jawo suka daga ƙasashen duniya kan laifukan yaƙi.
Isra'ila ta rusa duka unguwar Al Zeitoun mai gidaje fiye da 1,500 a Birnin Gaza
Isra'ila ta rusa duka unguwar Al Zeitoun mai gidaje fiye da 1,500 a Birnin Gaza / AFP
8 awanni baya

Tun bayan fara kai hare-haren kasa a wannan watan, Isra'ila ta rusa gidaje fiye da 1,500 a unguwar Al Zeitoun da ke birnin Gaza, in ji Hukumar Kula da Agajin Fararen Hula ta Falasdinawa.

Mahmoud Bassal, mai magana da yawun hukumar, ya bayyana cewa babu wani gini da ya rage a tsaye a kudancin unguwar bayan Isra'ila ta amince da shirin mamaye Gaza tun farkon wannan watan.

Sojojin Isra'ila sun yi amfani da manyan injinan gine-gine tare da na'urorin fasa abubuwa masu dauke da bama-bamai, suna tarwatsa wurare guda bakwai a kowace rana, tare da amfani da jiragen sama marasa matuƙa don jefa bama-bamai a saman rufin gidaje, in ji Bassal.

Ya kara da cewa, wadannan makamai sun kara tsananta girman barnar da aka yi a yankin.

Rusa gidajen da aka yi ya tilasta wa kashi 80 cikin 100 na mazauna Al Zeitoun yin hijira zuwa yammaci ko arewacin birnin Gaza, in ji Bassal.

A ranar 8 ga watan Agusta, Majalisar Tsaron Isra'ila ta amince da wani shiri na mamaye birnin Gaza.

Shirin ya kunshi korar Falasdinawa kusan miliyan daya zuwa kudu, da kewaye birnin, sannan da mamaye shi bayan kai hare-hare masu tsanani.

Isra'ila ta kashe kusan Falasdinawa 63,000 a Gaza tun watan Oktoba 2023.

Yakin ya lalata yankin, wanda ke fuskantar yunwa da Isra'ila ta kakaba masa.

A watan Nuwamba na bara, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da takardar kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant saboda laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza.

Haka kuma, Isra'ila tana fuskantar shari'ar kisan kare dangi a Kotun Duniya kan yakin da ta yi a yankin.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us