Ƙungiyar Haɗin kan Ƙasashen Musulmi ta OIC ta yi watsi da shirin Isra'ila na mamaye Gaza gaba ɗaya, tana mai kira da a ƙara matsa wa Tel Aviv lamba kan ta dakatar da hare-haren da take kai wa Falasɗinawa a yankin.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Linitin bayan taron gaggawa na ministocin da aka yi a Jeddah na ƙasar Saudiyya, ƙungiyar OIC ta yi kakkausar suka ga shirin Isra'ila na "mamaya da kuma amfani da ƙarfin soji a Zirin Gaza," tare da yin watsi da "duk wani shiri, ba tare da la'akari da yanayinsu ba, da ke da nufin korar al'ummar Falasɗinu da ƙarfin tsiya."
Ƙungiyar ta ɗora alhakin yaƙin da ake ci gaba da yi kan Isra'ila gaba ɗaya tare da yin watsi da shirye-shiryen kwantar da hankula da gangan saboda ƙin mayar da martani ga sabon kuɗurin tsagaita buɗe wuta na Gaza da Hamas ta amince da shi.
‘‘Tsarin na iya haifar da wata muhimmiyar yarjejeniya mai matukar tasiri don sakin waɗanda aka yi garkuwa da su da sauran mutanen da aka kama, tare da cim ma matsaya kan tsagaita wuta da kuma tabbatar da shigar da kayan agaji cikin gaggawa don magance bala’in jinƙai a Gaza,’’ in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta OIC ta kuma yi watsi da bayanan baya bayan nan da Firaiministan Benjamin Natanyahu ya yi kan abin da ya kira ‘‘Greater Isreal’’ a matsayin "tsawaita kalaman tsattsauran ra'ayi, da tunzura jama'a, da cin zarafi tare da take 'yancin kai na ƙasashe," da kuma keta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.
‘‘Greater Isreal’’ wata kalma ce daga Littafin Mai-Tsarki na Bible da aka yi amfani da ita a siyasar Isra’ila da nufin faɗaɗa yankin Isra’ila don haɗawa da Yammacin Kogin Jordan da Gaza da Tuddan Golan na Syria da yankin Sinai na Masar da kuma wasu sauran sassan Jordan.
Ƙungiyar ta OIC ta zargi Isra'ila da yin zagon ƙasa ga batun samar da ƙasashe biyu ta hanyar amincewa da wani babban aiki mai suna E1, wanda ya raba yankin yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye gida biyu tare da mayar da yankin gabacin Kudus da ta mamaye saniyar ware.
Kungiyar ta ƙasashen Musulmai ta kuma yi Allah wadai da harin da Isra'ila ke kai wa 'yan jarida da ƙwararrun kafafen yada labarai da gangan a Gaza.
"Waɗannan ayyukan sun zama laifin yaki da cin zarafi kan 'yancin 'yan jarida," a cewar OIC.
Ta yi ƙira ga dukkan ƙasashe ‘‘ da su ɗauki matakan da suka dace na doka masu tasiri,’’ ciki har da sanya takunkumi, da dakatar da jigilar makamai da kuma nazari kan alakar diflomasiyya da ta tattalin arziki, ‘‘don hana Isra’ila ci gaba da ayyukanta kan al’ummar Falasɗinu.’’
Sanarwar ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gaggauta ɗaukar matakin da ya dace bisa "ayyukan shari'a da na jinƙai karkashin sashi na VII na dokar Majalisar" don dakatar da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Falasɗinawa.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa sama da 62,700 a Gaza tun daga watan Oktoban 2023, kazalika hare-haren da sojoji suka kai ya lalata yankin da ke fuskantar yunwa.
A watan Nuwamban bara, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kame Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant bisa laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Har ila yau Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan kiyashi a kotun ƙasa da ƙasa kan yakin da ta ke yi da yankin.