Wani sabon rikicin ƙabilanci a arewacin Ghana da ya fara a ƙarshen watan jiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 31 tare da raba kusan dubu 50 da muhallansu, kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Alhamis, yayin da fiye da 13,000 suka tsallaka kan iyakar ƙasar zuwa Cote d'Ivoire.
A ranar 24 ga watan Agusta ne rikicin yankin Savannah na ƙasar Ghana ya ɓarke a ƙauyen Gbiniyiri da ke kusa da iyakar ƙasar Cote d’lvoire sakamakon taƙaddama kan filaye tsakanin wasu al’ummomi goma sha biyu.
Rikicin ya fara ne lokacin da shugaban yankin ya sayar da wani yanki na fili ga wani kamfanin gine-gine mai zaman kansa ba tare da izinin jama'a ba. A lokacin da kamfanin ya yi ƙoƙarin soma aiki a filin sai mazauna yankin suka yi turjiya kana suka hana shi shiga filin da ƙarfin tsiya.
Tashin hankalin ya kai ga ƙona fadar shugaban yankin da wuta.
Mata da yara ne lamarin ya fi shafa
Ministan Cikin Gida na Ghana Mubarak Muntaka ya faɗa a wata hira da ya yi da wani gidan radiyo a ranar Alhamis cewa, ‘yan Ghana dubu 13,253 ne suka tsallaka zuwa ƙasar Cote d’Ivoire, yana mai nuni kan wasu alƙaluman hukumomin Cote d’Ivoire.
"Akwai mutane 13,000 da suka isa ƙauyuka 17" a yankin, wanda tuni ya kasance matsuguni na 'yan gudun hijira 30,000 ‘yan Burkina Faso, kamar yadda Philippe Hien, shugaban majalisar yankin Bounkani ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
Hukumar kula da bala'o'i ta Ghana (NADMO) ta ce kimanin mutane 48,000 ne aka tilasta wa barin gidajensu, galibinsu kuma mata da yara ne.
"Ba a kai mana wani hari ba, kwana biyar ke nan kawo yanzu,’’ kamar yadda daraktan hukumar NADMO na yankin Savannah Zakaria Mahama ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.
An soma samun kwanciyar hankali
Shugabannin biyu Mahama da Muntaka sun tabbatar da mutuwar mutane 31.
A ɓangaren tsaro kuwa Muntaka ya ce an tura jam'i’an soji da ‘yan sanda fiye da 700 zuwa yankin tare da sanya dokar hana fita.
Ministan yankin Savannah Salisu Bi-Awuribe, ya ce sannu a hankali an soma samun zaman lafiya, la’akari da yadda sarakuna da dattawa yankin ke aiki tare da hukumomin tsaro domin hana sake ɓarkewar wani rikici.
Kazalika, an kafa kwamiti wanda ya haɗa sarakunan gargajiya da majalisar zaman lafiya ta ƙasa domin binciken musabbabin rikicin da kuma inganta hanyoyin sasantawa da zaman lafiya.