AFIRKA
6 MINTI KARATU
Abin da ya sa ya zame wa Afirka dole ta dauki matakin cimma wadatuwar abinci
Batun ‘yancin kai wajen samar da abinci ya kasance wani babban abin damuwa ga kasashen Afirka da dama.
Abin da ya sa ya zame wa Afirka dole ta dauki matakin cimma wadatuwar abinci
Wani mutum na sayar da kayan abinci a Afrika/AA / Others
12 Mayu 2023

Ranar 4 ga Fabrairu, shugaban Senegal Macky Sally ya yi kira da babbar murya ga kasarsa mai al’umma miliyan 17, don a cimma matakin dogaro da kai wajen samar da abinci.

A yayin wani taro na hukuma ya ce, “Idan muna so mu samu kariya daga matsalolin cinikin duniya, ba zai yiwu mu ci gaba da shigo da abinci mai dumbin yawa cikin kasarmu haka ba.”

Wannan wani kira ne da ya shafi daukacin Afirka, wadda ita ce nahiya ta biyu mafi yawan al’umma a duniya, mai mutum miliyan 249 da ke fama da yunwa a bisa kiyasi daban-daban.

Wannan adadi shi ne kashi 30 cikin 100 na jumullar masu fama da yunwa a fadin duniya.

Kiran na shugaban Senegal ya yi tsinkaye kan damuwa da kuma tsananin bukatar da ake da ita ga shugabannin Afirka wajen tabbatar da wadatuwar abinci ga ‘yan kasashensu, duba da yanayin rashin tabbas da duniya ke ciki.

A karshen watan Janairu, shugabannin kasashe, da manyan ‘yan kasuwa, da wakilan kungiyoyin gamayya, da kungiyoyin sa-kai, har ma da masana kimiyya da masu bincike, sun hadu a babban birnin Senegal don halartar taron koli karo na biyu kan samar da isasshen abinci.

Taken wannan taron koli na Dakar karo na biyu shi ne “Ciyar da Afirka: ‘yancin-kai da juriya wajen samar da abinci”.

Wannan taken ya tattaro matsalolin Afirka, yayin da duniya ke fuskantar barazanar karancin abinci saboda matsalar sauyin yanayi da rikicin Rasha da Ukraine, gami da burin gina cibiyar samar da abinci ta duniya a Afirka.

Haka nan shugaban Senegal shi ne ya gabatar da babban kuduri kan Afirka na burin habaka samar da abinci, maimakon dogara kan shigar da shi daga kasashen waje, ko kuma daga taimakon jin kai.

A karshen taron kolin na kwanaki uku, masu jibintar harkokin ci gaba sun yi alkawarin ware dala biliyan 30 don inganta samar da abinci a Afirka cikin shekaru biyar masu zuwa, a ta bakin Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka.

Batun ‘yancin kai wajen samar da abinci ya kasance wani babban abin damuwa ga kasar Senegal. Kasancewar kashi 72 na al’ummar kasar masu harkar noma ne, harkokin noma suna taka babbar rawa a tattalin arzikin kasar.

Sai dai Senegal wadda ke yankin Sahel kuma take gabar tekun Atlantika, tana shigar da kashi 70 na abincin da take bukata, yawanci shinkafa da alkama da kuma masara.

Wannan dogaro kan abinci daga waje yana daure wa mutane kai, ganin cewa kasar tana da gagarumar damar cimma bukatunta na samar da abinci da kanta.

Alal misali, yankin Senegal River Valley, wanda shi ne cibiyar da aka kai wa dauki a shirin Delta Land Development (SAED), yanki ne da ya kunshi wani sanannen waje da ke aka kiyasta cewa ya kai girman kadada 240,000 na filin noma.

Daga cikin wannan fadi, kadada 121,000 kawai ake amfani da ita a halin yanzu.

Kari kan wannan shi ne kasantuwar albarkatun yankuna masu ruwa da kasar take da shi, hada da yawan al’umma majiya karfi, da kuma kungiyoyin noma masu tsarin gudanarwa mai inganci.

A ta bakin Aboubacry Sow, Babban Daraktan SAED, yankin River Valley kadai yana da yalwar da zai iya samar wa kasar “isasshen abincin da zai wadaci al’ummarta”.

Sai dai kuma, yanayin da ake ciki a yanzu ba ya karfafa gwiwa.

A cewar wani nazari na Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP), kusan kashi 16 cikin 100 na al’ummar Senegal suna cikin matsalar rashin samun wadataccen abinci.

A 2013, shekara daya bayan shugaba Macky Sal ya hau mulki, an sanya Senegal a mataki na 154 cikin kasashe 186 a ma’aunin Ingancin Cigaban Mutane na duniya, wato Human Development Index (HDI).

A kasar da tattalin arzikinta ya fi dogara kan kamun kifi, da yawon bude-ido ko samar da gyada, wadda ita ce babban abin da ke samar mata da kudin shiga, ana bukatar wani babban sauyi musamman a fannin harkokin noma da kiwo.

Bayan la’akari da damar da kasar take da shi, shugaban Senegal ya kaddamar da shirye-shirye daban-daban da suka hada da babban shirin nan na Zaburar da Cigaban Harkokin Noma a Senegal na PRACAS II.

Makasudin wannan shiri shi ne cimma wadatuwa da kai wajen samar da shinkafa a kasar kafin shekara ta 2017. An jinkirta wa’adin shirin zuwa 2019, amma har farkon 2023 ba a yi kusa da cimma burin ba.

Babban abin lura daga taron koli na Dakar shi ne abin da aka ji daga bakin Akinwumi Adesina, shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka.

Ya fada wa shugabannin Afirka cewa, “Afirka ba ta da zabi saboda lokaci yana kure mana, idan kuka lura da karuwar yawan al’umma a nahiyar.”

“Ya zama wajibi mu dauki kwakkwaran mataki yanzu don cimma burin wadatuwar abinci. Hakan na bukatar karin tsare-tsaren samar da abinci mai tasiri da inganci da gogewa da kiyaye muhalli.

"Dole harkokin noma da kiwo su zama tamkar su ne man fetur a Afirka. Lokacin da Afirka za ta dau mataki yanzu ne kuma a nan ne."

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us