DUNIYA
3 MINTI KARATU
Isra'ila ta ce za ta janye jami'anta daga tattaunawar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Qatar
Wannan shafin ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Isra'ila ta ce za ta janye jami'anta daga tattaunawar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Qatar
Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza tun daga ranar Juma'a bayan an kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta. / Hoto:Others
2 Disamba 2023

1345 GMT — Isra'ila ta ce za ta janye jami'anta daga tattaunawar yarjejeniyar tsagaita wuta ta Qatar

Isra’ila ta ce za ta janye jami’anta na Mossad daga Qatar wadanda ke aikin tattaunawa da Hamas domin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a hare-haren da take ci gaba da kaiwa cikin Gaza.

“Bayan irin dambarwar da aka samu a tattaunawar da ake yi da kuma umarnin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayar, shugaban Mossad David Barnea ya bayar da umarni ga jami’ansa da ke Doha su koma Isra’ila,” kamar yadda ofishin firaiministan ya bayyana a wata sanarwa.

0930 GMT — Isra'ila ta kai hare-hare sama da 400 a Gaza a kwana guda

Sojojin Isra'ila sun kai hari sama da 400 a zirin Gaza da aka mamaye a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kamar yadda sojojin suka bayyana.

“A jiya [Juma’a], Hamas ta saba yarjejeniyar tsagaita wuta, domin mayar da martani, sojojin Isra’ila sun ci gba da yaki,” kamar yadda rundunar sojin ta Isra’ila ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.

Sojojin sun ce sun kai har “a wurare sama da 50 a Khan Yunis.”

Sama da Falasdinawa 15,000 Isra’ila ta kashe wadanda akasarinsu yara ne da mata tun daga 7 ga watan Oktoba bayan harin ba-zata da Hamas din ta kaddamar.

0850 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 240 tun bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta

Kungiyar Hamas ta ce mutum 240 aka kashe a Gaza da ke Falasdinu tun bayan da aka kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a ranar Juma'a.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an raunata karin mutum 650 a "daruruwan hare-hare ta sama da makaman atilare da bama-bamai daga sojojin ruwa a Zirin Gaza", in ji sanarwar,

Sanarwar ta ce sojojin na Isra'ila sun mayar da hankali wurin kai hare-hare a Khan Younis inda aka lalata gomman gidaje da mazauna cikin gidajen.

MAJIYA:AA, AFP, AP, Reuters
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us