Wani sabon bincike ya gano cewa kashi 60 cikin 100 na matasan Gen Z a Amurka suna goyon bayan ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas, fiye da Isra'ila a yaƙin da ake yi a Gaza.
A cikin jerin tambayoyi da aka yi, an tambayi masu amsa ta intanet: "A rikicin Isra'ila da Hamas, wa kuka fi goyon baya, Isra'ila ko Hamas?"
A cewar binciken da aka fitar a wannan makon, kashi 60 cikin 100 na matasa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 24 sun nuna goyon baya ga Hamas fiye da Isra'ila.
Daga cikin rukunin shekarun da suka fi goyon bayan Isra'ila akwai masu shekaru 25-34 da kashi 65 cikin 100, 35-44 da kashi 70 cikin 100, 45-54 da kashi 74 cikin 100, 55-64 da kashi 84 cikin 100, da kuma masu shekaru 65 da sama da kashi 89 cikin 100.
Binciken ya kuma gano cewa masu kada kuri'a sun kasu gida biyu kan ko Isra'ila tana aikata kisan kare dangi a Gaza, inda aka samu kunnen doki wato 50-50
Damuwa kan hakkokin dan Adam na Falasdinawa
Binciken ya kuma bayyana cewa mafi rinjayen masu amsa tamboyoyin (kashi 51 cikin 100) sun yi imani cewa caccakar da ake yi wa Isra’ila ya samo asali ne daga damuwa kan hakkokin dan Adam na Falasdinawa fiye da ƙin jinin Yahudawa.
An gudanar da binciken ne ta hanyar The Harris Poll da HarrisX tsakanin 20 zuwa 21 ga watan Agusta inda masu kada kuri'a 2,025 suka yi rajista, tare da kuskuren kashi 2.2 cikin 100. Binciken ya samu karbuwa sosai a matsayin shaida na sauyin ra'ayin jama'ar Amurka.
Harin Isra'ila ya kashe Falasdinawa kusan 63,400 tun watan Oktoban 2023, inda ya lalata yankin yayin da yunwa ke kara yaɗuwa a shekara ta biyu na kisan kare-dangi.
A watan Nuwamban da ya gabata, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta fitar da takardar kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant kan laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama.
Isra'ila tana kuma fuskantar shari'ar kisan kare dangi a Kotun Duniya kan yakin da take yi a yankin.