AFIRKA
2 MINTI KARATU
Kotu ta yanke wa sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami hukuncin kisa
Kotun wadda ke zama a Potiskum ta yanke hukuncin ne a ranar Talata bayan ta samu Lance Corporal John Gabriel da laifin kisan malamin.
Kotu ta yanke wa sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami hukuncin kisa
Sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya da motarsa kirar Honda kn hanyar Kano zuwa Gashuwa. / Hoto: Goni Aisami / Others
6 Disamba 2023

Kotu a Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta yanke wa sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun wadda ke zama a Potiskum ta yanke hukuncin ne a ranar Talata bayan ta samu Lance Corporal John Gabriel da laifin kisan malamin.

Mai Shari’a Usman Zanna Mohammed ne ya sanar da hukuncin kisan kan Gabriel wanda a baya ke karkashin Bataliya ta 241 da ke Nguru.

Sannan kuma alkalin kotun ya yanke wa Lance Corporal Adamu Gideon hukuncin daurin shekara goma a gidan yari sakamakon samunsa da laifin hadin baki.

Kotun ta ce ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta yi dogon nazari kan irin hujjojin da aka gabatar a gabanta wadanda suka gamsar da ita.

Sojojin da aka kama da laifin sun kashe fitaccen malamin ne bayan ya rage musu hanya da motarsa kan hanyar Kano zuwa Gashuwa.

Sheikh Goni Aisami fitaccen malami ne ɗan asalin garin Gashuwa a Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Kafin rasuwarsa, Sheikh Goni Aisami fitaccen malamin Addinin Musulunci ne a Nijeriya daga garin Gashuwa na Jihar Yobe wanda yake gudanar da tafsirin Al-Kur’ani a fadar Sarkin Gashuwa da kuma sauran wurare.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us