AFIRKA
2 minti karatu
Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a ƙauyuka da dama na Sudan
Ɗaruruwan mutane sun rasa muhallansu a Jihar River Nile sannan gomman gine-gine sun rushe sakamakon ruwan sama mai ƙarfi.
Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje a ƙauyuka da dama na Sudan
Mutane shida sun rasu lokacin da gidaje suka rushe sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a arewacin Jihar River Nile. / Getty
12 awanni baya

Akalla mutane 14 sun rasa rayukansu sakamakon ruwan sama mai karfi da ambaliyar ruwa a arewaci da kudu maso gabashin Sudan, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka bayyana a ranar Laraba.

Shaidu sun ce ruwan sama mai ƙarfi da ambaliyar ruwa sun lalata garuruwa da ƙauyuka da dama a Jihar River Nile, wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki da kuma rushewar gine-gine da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na jihar, SUNA, ya ruwaito.

Mutane shida sun rasu lokacin da gidaje suka rushe sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a arewacin Jihar River Nile.

Wata uwa da 'ya'yanta uku sun mutu a Jihar Sennar da ke kudancin Sudan bayan ɗakin gidansu ya rushe sakamakon ruwan sama mai karfi.

Mutane sun rasa matsuguni

Kwamitin Likitocin Sudan na Tsakiya ya bayyana cewa gidaje 154 sun lalace a Jihar River Nle, wanda ya tilasta wa mutane 1,078 barin gidajensu.

Kwamitin ya yi kira ga hukumomin yankin da kungiyoyin agaji da su gaggauta samar da abubuwan bukatu na gaggawa ga mutanen da abin ya shafa.

Sudan na yawan fuskantar ruwan sama mai yawa daga watan Yuni zuwa Oktoba, inda ƙasar ke fama da ambaliyar ruwa mai tsanani a kowace shekara.

Wannan bala'in na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yaƙin basasa tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF tun a watan Afrilun 2023. Wannan rikici ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma raba miliyoyin mutane da matsugunansu.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us