1523 GMT –– Yawan waɗanda hare-haren Isra'ila suka kashe a Gaza ya kai 18,205
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin Falasdinu ya karu zuwa akalla 18,205.
Kimanin mutum 49,645 ne suka samu raunuka tun a ranar 7 ga watan Oktoba, in ji kakakin ma'aikatar Ashraf al Qudra a cikin wata sanarwa.
1420 GMT –– Rundunar sojin Isra'ila sun ce an kashe mata sojoji biyar a kudancin Gaza
Sojojin Isra'ila biyar ne suka mutu a wani harin kwanton ɓauna da kungiyar Hamas ta kai a garin Khan Younis da ke kudancin Gaza, kamar yadda rundunar sojin ta sanar.
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce an kashe sojojin na bataliya ta 5 ne a lokacin da wani bam ya tashi a kusa da wata makaranta a birnin.
A cewar rundunar, an yi amfani da jirage masu saukar ungulu da jiragen yaki domin kai farmaki kan ‘yan bindigar Falasdinawa da suka bude wuta daga makarantar.
1208 GMT –– Isra'ila tana jefa wa dakarunta kayayyaki ta jirgin sama a kudancin Gaza
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta jefa wa dakarunta kayayyakin yaƙi daga jirgin sama a birnin Khan Younis a kudancin Gaza, yayin da ake ci gaba da gwabzawa tsakaninsu da mayaƙan ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa.
"A kwanakin da suke wauce, an yi jefa wa dakaru kayayyaki ta sama da suka haɗa da ton bakwai na kayayyakin yaƙi da na sauran buƙatu ga ɗaruruwan sojojin da ke fafatawa a Khan Younis," kamar yadda sanarwar sojin ta faɗa.
"Wannan ne karo na farko da aka jefa wa dakaru kayayyakin buƙata ta sama tun bayan Yaƙin Labanon" a 2016 in ji sanarwar.
0709 GMT –– Zanga-zanga kan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza ta durkusar da lamura a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Wata gagarumar zanga-zanga da aka gudanar a Gabar Yammacin Kogin Jordan don la'antar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza ta tsadar da komai a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
An tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a dukkan lardunan yankin, sannan an rufe ma'aikatu da bankuna da makarantu da shaguna da ma kasuwannin hada-hadar hannayen-jari, a cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Ana gudanar da zanga-zangar ce a wani bangare na gangami a fadin duniya domin nuna goyon baya ga al'ummar Gaza.
0200 GMT — Hamas ta ce mayakanta sun kashe sojojin Isra'ila 40 cikin awanni 48
Qassam Brigades, wato bangaren aikin soji kungiyar Hamas da ke fafatukar kare 'yancin Falasdinawa, ya sanar da kashe sojojin Isra'ila 40 da lalata motocin sojinsu 44 a awanni 48 da suka wuce.
“A cikin awanni 48 da suka wuce, mayakan Qassam sun lalata motocin soji 44 daga kowacce kusurwa da ake yaki a Gaza,” kamar yadda suka yi karin bayani a manhajarsu ta Telegram.
“Mayakansu sun tabbatar da kashe sojojin Isra'ila 40 sannan sun jikkata gommai,” in ji kungiyar.
Sanarwar ta kara da cewa mayakan sun yi wa sojojin Isra'ila kofar-rago sannan suka lalata wata cibiya yaki ta Isra'ila tare da harba rokoki kan sojojin na Isra'ila.
Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan ikirari na Hamas ba.
0216 GMT — Kungiyar Malaman Musulunci ta duniya ta yi kira a yi zanga-zanga a fadin duniya don neman tsagaita wuta a Gaza
Kungiyar Malaman Musulunci ta duniya ta yi kira a gudanar da zanga-zanga a fadin duniya a ranar Litinin domin tilasta wa Isra'ila daina luguden wuta a Gaza.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta yi kira ga jama'a a fadin duniya, musamman Musulmai, su shiga zanga-zangar sannan ta nemi manyan kungiyoyin dunuya da jam'iyyu da mutane masu fada-a-ji su ci gaba da yin zanga-zanga har sai lokacin da Isra'ila ta daina kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza.
Ta ce ta lura da yadda kaurace wa kayan Isra'ila da kuma yunkurin kai kayan agajin jinkai suka yi tasiri amma duk da haka ta nuna gazawar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wurin tsayar da yakin.
Kungiyar ta bayar da shawarar sauya tsarin hawa kujerar-na-ki na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, tana mai cewa ya kamata tsarin ya kasance bisa yawan kuri'un da aka kada.
Ali al Qaradaghi, Sakatare Janar na kungiyar, ya jaddada cewa za su yi zanga-zargar ce domin goyon bayan Falasdinawa da kuma kira ga kasashen duniya su matsa lamba don daina yaki a Gaza.