Wasu lokuta suna zama har abada a cikin ƙwaƙwalwar uwa - dumin jikin jariri sabon haihuwa, kama ƙananan yatsun jariri. Abin bakin ciki, ga Lynette Atieno ‘yar kasar Kenya, yanayi ne da ya zo da sanyaya gwiwa saboda rashi.
A cikin kwanakin da aka haife shi cikin koshin lafiya, jikin jaririn Lynette ya yi rauni sosai, fatarsa ta yi saurin kode wa. Lokacin da ta isa asibiti mafi kusa, an riga an makara.
"Kwanakinsa bakwai kawai," Atieno ta shaida wa TRT Afrika, muryarta cike da karaya. "Likitoci sun ce cutar sepsis ce. Da sun sani da wuri, watakila da..."
Kalamanta sun sarkafe, sun nutse cikin shiru da wani irin bakin ciki mai karfi wanda hakan ya sa ta rasa me za ta ce ko yi.
Lynette ba ita kaɗai ba ce a cikin irin wannan mummunan yanayi. Cutar Neonatal sepsis na yin ajalin dubban jarirai a faɗin Afirka kowace shekara. A Najeriya, Amina Yusuf na fuskantar irin wannan radadi.
"Sun fada mani cewa jaririna yana dauke da ciwon, amma gwajin ya dauki lokaci sosai," in ji ta. "Ta riga ta tafi a lokacin da sakamakon ya fito."
Cutar sepsis, wadda a likitance aka bayyana a matsayin cuta mai barazana ga rayuka, cutar na janyo kashi 15% na mutuwar jarirai miliyan 2.3 da ke faruwa a duniya kowace shekara.
Galibin waɗannan mace-mace suna faruwa ne a ƙasashe masu karanci da matsakaicin kuɗi, inda kayan aikin gano cutar ba su da yawa, ko ake snah wahalar samun su, ko ma babu su gaba daya.
Muhimmin matakin cigaba
A ranar 6 ga Agusta, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da sabon bayani na matakan da ake son cim mawa (TPP) don jagorantar cigaban gwaje-gwaje cikin sauri, samar da ingantattun gwaje-gwaje na cututtukan da suka hada da sepsis da ke kama jarirai ‘yan kasa da watanni biyu da haihuwa.
Hanyoyin gano cutar a yanzu ba su da tasiriba su da tasiri a tsari da ba shi da isassun kayan aiki.
Gwajin tsarin jini da halitta na bukatar kayan gwaji na zamani, yana daukar kwanaki kafin a samu sakamako, kuma a wasu lokutan ma ba ya iya gano cutar a farkon kwanakinta.
Ba tare da tabbatattun kayan gwaji ba, yawancin ma'aikatan kiwon lafiya na dogara da bayyanar alamun cutar su kaɗai don tabbatar da akwai cutar, wanda ke haifar da jinkirin magance cutar ko amfani da ƙwayoyin maganin da ba su kamata a yi amfani da su ba. Ƙarauwar samun bijirewa magungunan da jiki ke yi ma wani ƙalubale ne.
"Gwajin bincike a kan lokaci kuma daidai don gano kwayoyin cutar da ke shiga jini na da matukar muhimmanci wajen rage mace-macen jarirai," in ji Dokta Yvan JF Hutin, daraktan sashen kula da riga-kafin cututtuka na WHO.
Tsarin kawo canji
Sabbin ka’idojin TPP sun fayyace yadda za a dinga yin gwaje-gwaje a nan gaba. Na farko dai dole ne su zama masu rahusa, masu bayar da sakamako da wuri kuma wadanda za a iya amfani da su har a asibitocin karkara.
Asali dai, waɗannan gwaje-gwajen za su baiwa ma'aikatan kiwon lafiya damar tantance wa cikin sa'o'i ko jariri yana buƙatar antibiotics ko kulawar asibiti cikin gaggawa.
Dr Silvia Bertagnolio, shugabar sanya ido kan bijirewar magunguna a WHO ta ce "Ganowar farko na iya nuna bambanci tsakanin rayuwa da mutuwa."
"Wannan ba kawai game da ingantattun gwaje-gwaje ba ne, ya shafi baiwa kowane jariri damar yin gwagwarmaya."
Ka'idojin na WHO na da manufa kai tsaye ga masana'antun samar da kayan gwaji, gwamnatoci da abokan aikin lafiya na duniya.
Yayin da lokaci ya yi nisa game da ƙalubalen canza wannan tsarin zuwa na gaske, iyaye mata masu baƙin ciki irin su Lynette da Amina suna fatan wasu ba za su sha irin wahalar da ke tattare da su ba a yau.
"Idan wata uwa ba za ta rasa jaririnta kamar yadda na yi ba, to watakila radadin da na ke ji bai tafi haka kawai ba," Lynette ta shaida wa TRT Afrika.