DUNIYA
4 MINTI KARATU
Ƴan kama-wuri-zauna su ne suke kawo matsala ga samar da ƙasar Falasɗinu — Erdogan
Shugaban Turkiyya ya soki Ƙasashen Yammacin Duniya kan goyon baya mara iyaka da suke bai wa Isra'ila a daidai lokacin da gwamnatin Firaministan Netanyahu ke aiwatar da kisan kiyashi a kan Falasdinawa a kwana 151 da ta shafe tana yaƙi a Zirin Gaza.
Ƴan kama-wuri-zauna su ne suke kawo matsala ga samar da ƙasar Falasɗinu — Erdogan
Kafin taron manema labarai, shugabannin biyu sun yi wata ganawa a harabar fadar shugaban kasar da ke Ankara babban birnin kasar Turkiyya /Picha: AA / Others
5 Maris 2024

"A cikin kwanaki 151 da suka gabata, muna shaida daya daga cikin mafi girman ɓarna a ƙarnin da ya gabata," in ji shugaban kasar Turkiyya Erdogan, yayin da yake ishara da yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza na Falasdinu.

A wani taron manema labarai da ya yi da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas a ranar Talata, shugaban na Turkiyya ya zargi gwamnatin Firaiminista Netanyahu na Isra'ila da yin kisan kare dangi a kan Falasdinawa, tare da samun goyon baya mara iyaka daga Ƙasashen Yammacin Duniya.

Erdogan ya ce "Netanyahu da wadanda ke da hannu a kisan za su fuskanci hukunci kan duk wani ɗigon jini da aka zubar a idon doka da al'ummar duniya."

Kafin taron manema labarai, shugabannin biyu sun yi wata ganawa a harabar fadar shugaban kasar da ke Ankara babban birnin kasar Turkiyya, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu, da batun Gaza, da kuma harkokin yankin.

Da yake nanata cewa hanya daya tilo ta samun zaman lafiya mai dorewa ita ce kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta tare da Gabashin Ƙudus a matsayin babban birninta a cikin iyakokin shekarar 1967, ya bayyana cewa, "Ayyukan Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna wadanda a haƙiƙa sun mamaye yankunan Falasɗinawa, na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga samun mafita."

A yayin taron manema labarai, Shugaba Erdogan ya kira bukatun 'yan siyasa masu tsattsauran ra'ayi na Isra'ila na hana Musulmi shiga Masallacin Ƙudus da cewa "shirme ne muraran".

Ta'addancin da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza

A ranar Alhamis din da ta gabata ne sojojin Isra'ila suka bude wuta kan taron jama'ar Falasdinawa da ke jiran agajin jinƙai a unguwar Al Nabulsi da ke kan titin Al Rashid, wata babbar hanyar gabar teku zuwa yammacin birnin Gaza a arewacin Gaza.

Harin ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 112 tare da jikkata wasu 760.

Isra'ila ta kaddamar da wani kazamin farmakin soji kan yankin Falasdinawa da ta yi wa ƙawanya tun bayan harin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda Tel Aviv ta ce ta kashe 'yan Isra'ila kusan 1,200.

Yakin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 151, inda aka kashe Falasdinawa akalla 30,534, galibi yara da mata, tare da jikkata wasu 71,980.

Har ila yau Isra’ila ta ƙaƙaba wani shingen hana fita a Gaza, lamarin da ya bar al’ummarta, musamman mazauna arewacin Gaza a yanayi na gab da fadawa cikin yunwa.

Yakin Isra'ila ya mayar da kashi 85% na al'ummar Gaza ƴan gudun hijira a cikin yankinsu, cikin yanayi na matsanancin karancin abinci da ruwan sha mai tsafta, da magunguna, yayin da kashi 60% na ababen more rayuwa na yankin suka lalace, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Ana tuhumar Isra'ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya.

Wani hukunci na wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da ayyukan kisan kiyashi tare da daukar matakan tabbatar da cewa ana ba da taimakon jinƙai ga fararen hula a Gaza.

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us