KASUWANCI
2 MINTI KARATU
Kamfanin samar da takalman sanyi na Dr Martens ya sanar da dan Nijeriya a matsayin shugabansa
Ije Nwokorie ne sabon shugaban zartarwa na kamfanin samar da takalman sanyi manya na Dr Martens, a yayin da Kenny Wilson ya bayyana daga wannan shekarar zai sauka daga kan shugabancin kamfanin.
Kamfanin samar da takalman sanyi na Dr Martens ya sanar da dan Nijeriya a matsayin shugabansa
Wata mace ke wuce wa ta bakin shagon Dr Martens, Birtaniya. Hoto / Reuters / Others
16 Afrilu 2024

Kamfanin Dr Martens ya sanar da shugaban sashen tallata kamfanin Ije Nwokorie a matsayin sabon shugaban zartarwarsu (CEO), bayan da Kenny Wilson ya yanke shawarar hakura da shugabancin kamfanin samar dantakalman na Birtaniya a ranar Talata.

Nwokorie asalin dan Nijeriya ne. Kamfanin bai bayyana tsayayyiyar ranar miƙa masa jagorancin kamfanin ba.

Dr Martens ya sanar da saukar hannun jarinsa da kashi 30 a ranar Talata wanda faduwa ce msfi girma tun bayan da kamfanin na Birtaniya da ke samar da takalma sau ciki ya yi gargadi kan tunkarar shekara mai wahala a kasuwannin Amurka, wanda hakan babban kalubale ne ga sabon shugaban.

Kamfanin na fama da karancin masu sayen takalmansa a Amurka musamman masu sayen sari.

Sakamako mara kyau

Hannun jarin kamfanin ya fuskanci tarnaki a ‘yan shekarun nan, kuma hakan ya janyo abokin huldarsa na Marathon yin gargadi da kira da a samar da sabbin dabarun kasuwanci a farkon wannan watan.

A kasuwancin ranar Talata kamfanin ya fuskanci tangardar raguwar sayayya da kaso 65.5.

Dr Martens y ace sakamakonsa na wannan shekarar ya kare a ranar 31 ga Maris 2024, kuma suna fuskantar sabuwar shekara mai tsauri.

A wata sanarwa ta daban da kamfanin ya fitar y ace, sakamakonsu na kudade na 2024 zai yi daidai da tsammanin da ake yi musu.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us