DUNIYA
7 MINTI KARATU
An gano gawarwaki da dama a Khan Younis bayan janyewar dakarun Isra'ila
Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ɗin nan ya shiga kwana na 298, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,363  — galibinsu  mata da yara –– sannan ya jikkata mutum 90,923, kana an yi amanna sama da mutum 10,000 na danne a ɓaraguzai.
An gano gawarwaki da dama a Khan Younis bayan janyewar dakarun Isra'ila
An gano gawarwaki da dama a Khan Younis bayan janyewar dakarun Isra'ila / Photo: Reuters
30 Yuli 2024

1436 GMT — Isra'ila da Hizbullah sun yi musayar wuta duk da kiraye-kirayen dakatawa

Isra'ila da kungiyar Hizbullah sun yi musayar wuta mai muni, bayan harin roka da aka kai daga kasar Labanon duk da kiraye-kirayen dakatawa da ake musu.

Likitocin Isra'ila sun ce an kashe wani mutum mai shekaru 30, bayan wani harin roka da aka kai a Kibbutz na arewacin HaGoshrim.

A halin da ake ciki sojojin Isra'ila sun ba da rahoton cewa dakarun nasu da ke Lebanon suna "kai hari da yin ɓarin wuta".

A baya-bayan nan dai ta bayyana cewa, ta kai hare-hare kimanin 10 kan mayakan Hizbullah a cikin dare a yankuna bakwai daban-daban na kudancin kasar Lebanon, inda suka kashe daya daga cikin mayakan kungiyar da ke samun goyon bayan Iran.

1150 GMT — An gano gawarwaki da dama a Khan Younis bayan janyewar dakarun Isra'ila

Ma'aikatan Lafiya na Falasɗinu sun gano gawarwaki na aƙalla mutum 42 a Khan Younis da ke kudancin Gaza, bayan da akarun Isra'ila suka janye daga yankin, a cewar hukumomin wajen.

Shugaban ofishin watsa labarai na gwamnatin Gaza Ismail Thawabta ya ce, an gano gawarwakin mutum 42 da aka kashe a cikin sa'o'i kadan da suka gabata.

"Muna sa ran adadin wadanda suka mutu zai ƙaru saboda har yanzu akwai gawarwaki da dama a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin," in ji shi.

Talata, 30 ga watan Yuli, 2024

0953 GMT ––Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari a wurare kusan 10 da ke yankuna bakwai daban-daban na ƙungiyar Hezbollah a kudancin Lebanon, inda ta kashe mayaƙin ƙungiyar guda ɗaya.

Kazalika sojojin sun "kai hari a ma'ajiyar makamai ta Hezbollah da kayan sojoji da na'urar kai hari a kudancin Lebanon".

0214 GMT ––Lebanon ta ɗaura ɗamarar yaƙi yayin da jami'an diflomasiyya ke ƙoƙarin yin sulhu tsakanin Isra'ila da Hezbollah

Ministan Harkokin Wajen Lebanon Abdallah Bou Habib ya ce ana ci gaba da neman hanyoyin diflomasiyya na hana ɓarkewar gagarumin yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu.

"Isra'ila za ta kai hari mara yawa kuma ita ma Hezbollah za ta yi martani mara yawa... Wannan shi ne tabbacin da muka samu," in ji Bou Habib a hira da kafar watsa labarai ta Al-Jadeed.

Masu sharhi da dama sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP mai yiwuwa maganar da ministan ya faɗa ita ce za ta faru, domin kuwa Isra'ila ba za ta so tsunduma cikin yaƙe-yaƙe biyu a lokaci guda ba.

Amurka da Faransa da wasu ƙasashe suna ƙoƙarin hana dagulewar lamura tsakanin ɓangarorin biyu, a cewar Habib, yayin da Firaministan Lebanon Najib Mikati ya ce "ana tattaunawa da manyan ƙasashen duniya da na Turai ma kuma Larabawa domin kare Lebanon da kuma hana aukuwar wani bala'i".

2030 GMT — Hezbollah tana shirya makamanta masu linzami yayin da Isra'ila ta yi barazanar kai hari a Lebanon

Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta soma shirya makamanta masu linzami a yayin da Isra'ila ta yi barazanar kai hari a Lebanon sakamakon harin da aka kai a Tuddan Golan da ta mamaye wanda ya kashe yara 12 a ƙarshen mako.

Wani jami'i a Lebanon ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa matsayin Hezbollah bai sauya ba kuma ƙungiyar ba ta son a gwabza yaƙi gadan-gadan da Isra'ila wadda Amurka ke mara wa baya, amma idan yaƙin ya ɓarke za ta fafata ba tare da iyaka ba.

Jami'in, wanda ba ya so a ambaci sunansa kan lamuran da suka shafi harkar soji, ya ce tun ranar Lahadi Hezbollah ta soma shirya makamanta masu linzami da ke da ƙarfin aiki domin amfani da su idan buƙatar hakan ta taso.

Isra'ila ta ƙiyasta cewa Hezbollah tana da rokoki da makamai masu linzami kimanin 150,000, cikinsu har da waɗanda ke iya sauka inda aka aika su ba tare da yin kuskure ba. Hezbollah ta ce za ta ci gaba da gumurzu da Isra'ila har sai mahukunta a birnin Tel Aviv sun kawo ƙarshen kisan ƙare-dangin da suke yi a yankin Gaza da suka mamaye.

2000 GMT — Isra'ila tana shan suka bayan an fitar da wasu sabbin shaidu a kanta game da aikata laifukan yaƙi

Isra'ila na fuskantar sabuwar suka game da aikata laifukan yaƙi bayan an fitar da wasu sabbin bidiyoyi da ke nuna yadda dakarunta suke lalata wata ma'ajiyar ruwan sha a kudancin Gaza, tare da wasu rahotanni da suka nuna yadda sojojinta suka yi fyaɗe ga wata Bafalasɗiniya fursuna a gidan yari da ke Negev Desert.

Wani sojan Isra'ila na Runduna ta 401 da ke aiki a Rafah ya "lalata wata ma'ajiyar ruwa a makon jiya bayan ya samu umarni daga kwamandodjinsa," a cewar wani rahoto daga jaridar Haaretz da ake wallafawa a Isra'ila.

Kazalika wani sojan ya wallafa bidiyo a shafinsa na sada zumunta da ke nuna yadda aka "tarwatsa ma'ajiyar ruwa ta Tel Sultan domin bikin Shabbat," in ji jaridar.

A gefe guda, sojojin Isra'ila 1200 masu tsattsauran ra'ayi sun kutsa sansanin sojoji na Sde Teiman da ke saharar Negev inda ake tsare da sojoji tara saboda samunsu da laifin yin fyaɗe ga wata Bafalasɗiniya da aka yi garkuwa da ita.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us