DUNIYA
2 MINTI KARATU
Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas  Ismail Haniyeh kisan gilla a Iran
An kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh da ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa a Tehran, a cewar rundunar zaratan sojoji ta Iran wato Revolutionary Guards.
Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas  Ismail Haniyeh kisan gilla a Iran
Hamas ta ce Isra'ila ce ta kashe shugabanta ranar Laraba da sanyin safiya a samamen da ta kai a gidansa da ke Tehran. / Photo: AA / Others
31 Yuli 2024

An yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh kisan gilla a Iran, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar da kuma jami'an gwamnatin Iran suka fitar.

Hamas ta ce Isra'ila ce ta yi wa shugabanta kisan gilla ranar Laraba da sanyin safiya a samamen da ta kai a gidansa da ke Tehran.

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta bayyana juyayin rasuwar Haniyeh, mai shekara 62, wanda "miyagu masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra'ila" suka kashe a gidansa da ke Tehran.

Haniyeh, wanda fitacce ne a fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawam ya daɗe yana gwagwarmaya kan kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza.

Gwamnatin Iran ta ce ta ƙaddamar da bincike kan kisansa, wanda take sa ran fitar da sakamakonsa nan ba da jimawa ba.

"An kai hari a gidan shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, Ismail Haniyeh a Tehran, kuma sakamakon hakan shi da ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa sun yi shahada," in ji wata sanarwa da shafin intanet na Sepah, mallakin rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps ya wallafa.

Kawo yanzu babu wanda ya ɗauki alhakin kisan, sai dai ana zargin Isra'ila da aikata shi, domin kuwa ta daɗe da shan alwashin kashe Haniyeh da sauran shugabannin ƙungiyar Hamas.

MAJIYA:AA
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us