DUNIYA
6 MINTI KARATU
An yi jana'izar Haniyeh a Doha
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 301, kuma ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,480, galibinsu mata da yara tare da jikkata wasu 91,128. Sannan ana ƙiyasin wasu sama da 10,000 na binne a karkashin baraguzan gidajen da aka rusa.
An yi jana'izar Haniyeh a Doha
An rufe manya da ƙananan hanyoyi da dama da ke Doha, yayin da 'yan sanda suka ɗauki ƙarin matakan tsaro, musamman a kusa da Masallacin Imam Muhammad ibn Abd al-Wahhab, inda aka gudanar da jana'izar bayan Sallar Juma'a / Hoto: AFP / Others
2 Agusta 2024

Juma'a, 2 ga Agustan 2024

0945 GMT — Hukumomi a Qatar sun ɗauki tsauraran matakan tsaro a wajen jana'izar i shugaban ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh, wanda Isra'ila ta yi wa kisan gilla a Tehran, babban birnin Iran.

An fuskanci dogayen layuka tun daga Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Hamad da ke Doha tun tsakar dare a yayin da jami'ai daga ƙasashe da dama suka isa ƙasar don halartar jana'izar.

An rufe manya da ƙananan hanyoyi da dama da ke Doha, yayin da 'yan sanda suka ɗauki ƙarin matakan tsaro, musamman a kusa da Masallacin Imam Muhammad ibn Abd al-Wahhab, inda aka gudanar da jana'izar bayan Sallar Juma'a, a cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

'Yan jarida na cikin gida da ƙasashen waje sun taru a yankin domin ɗaukar labaran jana'izar.

0446 GMT — Kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas ba zai taimaka wa tattaunawar tsagaita wuta ba — Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh bai taimaka wa tattaunawar tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza ba.

An samu ƙaruwar zaman ɗarɗar a yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya bayan kisan gillar da aka yi wa Haniyeh a Iran inda ake fargabar ramuwar gayya kan Isra'ila.

Hamas da rundunar zaratan sojojin Iran ta Revolutionary Guard sun tabbatar da kisan Haniyeh, wanda yake shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza.

"Ba zai taimaka wa tattaunawar ba," in ji Biden a tattaunawa da manema labarai yayin da suka tambaye shi kan ko kisan Haniyeh zai tarwatsa tattaunawar tsagaita wuta.

Kazalika Biden ya ce ya tattauna da Firaministan Benjamin Netanyahu ranar Alhamis.

2145 GMT — Biden ya sha alwashin goyon bayan Netanyahu bayan harin makamai masu linzami da Hezbollah ta kai Isra'ila

Shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, yayin da Fadar White House ta fada a cikin wa jawabi cewa, Biden "ya jaddada aniyarsa na tabbatar da tsaron Isra'ila daga duk wata barazana daga Iran," ciki har da ƙawayenta Hamas da Hezbollah da Houthi.

Ita ma mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta halarci kiran wayar.

Biden ya kuma tattauna kan kokarin tallafa wa tsaron Isra'ila da kuma muhimmancin rage zaman ɗar-ɗar a yankin, duk da cewa ba a yi ƙasa a gwiwa ba wajen kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma kashe-kashen da ake yi a yankin da ya ƙara ruruta wutar rikicin yankin.

A cewar Cibiyar Bayar da Bayanai ta Armed Conflict Location and Event Event (ACLED), Isra'ila ce ke da alhakin kai hare-hare 17,081 a kasashe takwas tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara, ciki har da yankin Falasdinu da ta mamaye da Lebanon da Syria da Masar da Yemen da Jordan da Iran da kuma Iraƙi.

2000 GMT — An nemi Biden ya kawo ƙarshen shirun da ake yi kan yadda Isra'ila ke ƙwace yankuna da kisan kiyashi a Gaza

Majalisar Hulda da Musulman Amurka, CAIR, kuma babbar kungiyar kare hakkin Musulmai a Amurka, ta ce tilas ne gwamnatin Biden ta dauki mataki bayan da Isra’ila ta sanar da sake ƙwace kasar Falasdinu a Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye tare da kashe wasu fararen hula a Gaza.

Isra'ila ta sanar da ƙwace kusan kadada 2,000 ta kasar Falasdinu kusa da garin Salfit da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.

"Ci gaba da yin shiru da gwamnatin Biden ke yi kan kisan kiyashin da ake yi a kullum da sauran laifukan yaki a Gaza, da kuma batun mamaye Yammacin Kogin Jordan, yana aike wa da gwamnatin Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi cewa ba za ta taba daukar alhakin duk wani mataki da ta dauka ba, komai rashin dacewarsa a doka, "in ji Mataimakin Daraktan CAIR na kasa Edward Ahmed Mitchell.

"Dole a kawo ƙarshen wannnan shirun na kisan ƙare dangi."

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us