Asabar, 3 ga watan Agusta, 2024
1043 GMT — Jami’ai daga Isra’ila sun isa birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa kan musayar fursunoni da Hamas, kamar yadda gidan rediyon soji na Isra’ila ya tabbatar a ranar Asabar.
Wannan na zuwa ne a yayin da dangantaka ke ƙara tsami tsakanin Isra’ila da Hamas, inda a ɗayan ɓangaren kuma Isra’ila ke ƙara takun-saƙa da Hezbollah da Iran.
Haka kuma ana fargabar a ko wane irin lokaci Iran za ta iya mayar da martani kan Isra’ila bayan kisan da aka yi na shugaban Hamas Ismail Haniyeh a cikin Tehran.
0057 GMT — Isra'ila da Amurka suna shiri domin kauce wa "hare-hare na martanin da Iran za ta kai a kowane lokaci a ƙarshen makon nan," a cewar wani rahoto na jaridar Wall Street Journal.
"Babu tababa cewa hakan zai faru. Isra'ila ta wuce gona da iri. Martanin da za mu mayar zai kasance mai ƙarfi," in ji jaridar Journal wadda ta ambato wani jami'in diflomasiyyar Irann yana yin waɗannan kalamai.
Jami'in ya ce duk wata lalama daga ƙasashen duniya don kada Iran ta mayar da martani "ba za ta yi aiki ba" idan aka yi la'akari da hare-haren da Isra'ila ta kai a baya bayan nan.
Hakan na zuwa ne bayan da Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce an ba ta umarni ta tura jiragen ruwa na yaƙi da na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami yankin Gabas ta Tsakiya.
2142 GMT — Amurka ta tura jiragen ruwan yaƙi da manyan jirage da na'urorin kakkaɓo makamai Gabas ta Tsakiya
Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya bayar da umarni a tura jiragen ruwa na yaƙi da manyan jirage yankin Gabas ta Tsakiya bayan kisan gillar da Isra'ila ta yi a Iran da Lebanon, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon.
Kazalika Amurka ta aika da ƙarin tawaga ta jiragen sama na yaƙi da na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami, in ji Pentagon.
Amurka na ɗaukar waɗannan matakai ne domin tunkarar barazanar da Iran da ƙawayenta suka yi kan yin martani bayan kisan gillar da Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh kwana biyu da suka wuce a Tehran da kuma kisan da ta yi wa babban kwamandan Hezbollah a Beirut a yayin da take ci gaba da aiwatar da kisan ƙare-dangi a Gaza.
"(Austin) ya shaida wa ministan tsaron Isra'ila ƙarin matakan da ma'aikatar tsaro take ɗauka da suka haɗa da sauye-sauyen da za su tabbatar da tsaron Isra'ila," in ji kakakin Pentagon Sabrina Singh a yayin da take bayar da sanarwa ga manema labarai.
"Ta ƙara da cewa, "(Austin) ya tabbatar wa minista Gallant da Shugaba Joe Biden da kuma Firaminista Benjamin Netanyahu cewa za mu tura ƙarin matakan tsaro domin kare yankin."
2036 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 5, ciki har da yara 3, a Gaza
Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa biyar, ciki har da yara uku, a wani hari ta sama da ta kai gidansu a Birnin Gaza, a cewar Rundunar Kare Fararen-hula ta Falasɗinu.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce, "Tawagarmu ta gano gawawwaki biyar na shahidai, ciki har da yara uku, da kuma waɗanda suka jikkata, bayan jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari a gidan iyalan Abu Hasira a yankin Al-Sabra" da ke Birnin Gaza.
2000 GMT — Hamas na nuna shakku kan aniyar Netanyahu ta neman zaman lafiya bayan Isra'ila ta ce za ta tura wakilai Masar
Ƙungiyar da ke fafutukar kare Falasɗinawa ta Hamas ta bayyana shakku kan aniyar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ta neman zaman lafiya bayan ya ce zai tura tawaga Masar don tattaunawar tsagaita wuta.
"Netanyahu ba ya so a kawo ƙarshen yaƙin nan kuma yana yin kalaman da ba su da tabbas domin rufe laifukan yaƙin da yake aikatawa," a cewar wani babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri.
Abu Zhuri na bayani ne bayan wata sanarwa da ofishin Netanyahu ya fitar cewa: "Tawagar masu tattaunawa don yin fitar da waɗanda aka yi garkuwa da su za ta tafi birnin Alƙajira ranar Asabar da daddare ko Lahadi da safe."