Alhamis 8 ga Agustan 2024
1242 GMT — Isra'ila ta ba da umarnin kwashe mutane daga Khan Younis kafin wani sabon farmaki
Sojojin Isra'ila sun ba da sabbin umarnin kwashe fararen hula a kudancin Gaza na Khan Younis a shirye-shiryen kai wani sabon farmaki a yankin.
Kakakin soji Avichay Adraee ya yi kira ga mazauna garuruwan Salqa da al-Qarara da Bani Suheila da Abasan da Khuza'a da Sheikh Nasser da al-Satar da kuma al-Mahatta da su gaggauta ficewa zuwa abin da ya kira "yankin jinƙai" yammacin Khan Younis.
Kakakin ya yi ikirarin cewa Hamas na amfani da wadannan yankuna wajen harba rokoki zuwa Isra'ila.
0955 GMT — Yawan Falasɗinawan da aka kashe a Gaza sun kai 39,700
Ma'aikatar Lafiya ta Gaza ta ce aƙalla Falasɗinawa 39,699 aka kashe a yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Alƙaluman sun haɗa da mace-mace 22 da aka samu a cikin awa 24 da suka wuce, a cewar ma'aikatar, sannan kuma yawan wadanda aka jikkata ya kai 91,722 a Gazan tun daga 7 ga watan Oktoban bara.
0105 GMT —Tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza da musayar fursunoni ta ci tura - Kafar yada labaran Isra'ila
Tattaunawar da ake shirin yi kan musayar fursunonin da ake garkuwa da su da kuma tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinu a Gaza ta ci tura, ba tare da shirya gudanar da taro ba, in ji kafar yada labaran Isra'ila.
Kafar yada labaran gwamnatin Isra'ila ta KAN ce ta sanar da hakan tana mai ambatar wasu majiyoyin ƙasashen waje da ba ta bayyana sunansu ba.
Majiyoyin sun nuna cewa a halin yanzu an dakatar da batun ci gaba da tattaunawar kan yarjejeniyar da aka ƙulla.
Sakamakon haka, ba a kayyade wasu sabbin ranakun tattaunawa tsakanin shugabannin hukumomin tsaron Isra'ila da Qatar da Masar da Amurka ba.
Kazalika, KAN ta kuma rawaito cewa iyalan Isra'ilawan da ake garkuwa da su a Gaza waɗanda suka gana da tawagar sasantawa ta Isra'ila kwanan nan sun samu saƙonni marasa kyakkyawan fata game da yiwuwar samun cigaba a sasantawar.
Wakilan tawagar Isra'ila sun sanar da iyalan cewa "ba sa saka ran samun nasara a wannan shawarwarin nan gaba kadan."
An alakanta tattaunawar da ta tsaya cik ba wai kawai shirye-shiryen mayar da martani ga Iran kan kisan gillar da Isra'ila ta yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin kasar Iran a makon da ya gabata ba, har ma saboda rashin warware sabanin da aka samu kan matsayar Isra'ila kan batun.
2027 GMT — Netanyahu ya musanta ikirarin Amurka na samun ci gaba a tattaunawar sulhun Gaza
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya mayar da martani ga kalaman kakakin Majalisar Tsaron Amurka John Kirby kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka yi wa ƙawanya.
Netanyahu ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ba ta samu martani daga kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ba kan shirin tsagaita wuta da musayar fursunoni, duk kuwa da gabatar da wata "miƙaƙƙiyar shawara" tare da aikewa da tawagar sasantawa zuwa birnin Alkahira a ranar Asabar din da ta gabata.
Hakan ya faru ne bayan Kirby ya shaida wa manema labarai cewa "akwai shawara mai kyau a gaban bangarorin biyu, kuma suna bukatar dukkansu su amince da wannan shawara domin mu cim ma wannan wuri."
Amurka ta yi imanin cewa bangarorin biyu "suna bukatar yin wani aiki na karshe" don cim ma matsaya, in ji shi.