Maziko Matemba, wani mai fatutukar kula da lafiyar al’umma daga yankin Blantyre na Malawi ya ziyarci Amurka sau bakwai a shekaru goman da suka gabata.
Duk wadannan ziyara da ya kai na da alaka da dadilan aiki. Kuma bai taba wuce kwanakin da visa ta yarje masa ya zauna a kasar ba,
A karkashin sabbin dokokin shige da fice na Amurka, wadanda ake zaton na da manufar dakile karya sharuddan visa da ‘yan wasu kasashe ke yi, Matemba zai biya karin dala 15,000 a yayin d atafiya zuwa Amurka da zai yi a nan gaba.
Wannan adadin kudi ya haura yawan kudaden shiga na shekaru da dama da 'yan kasa da dama ke samu a wannan kasa ta kudancin Afirka mai yawan al'umma sama da miliyan 21.
A wajen hedkwatar gudun hijira ta Malawi da ke Blantyre, yawancin masu neman fasfo na shirin tafiya Amurka sun yi matukar kaduwa da abin da ake gani a matsayin makami na viza don sanya wani sharadin bayar da makudan kudade.
Dora laifi na rashin adalci
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da cewa sabuwar dokar da za ta fara aiki a ranar 20 ga watan Agusta, ta shafi wadanda ke tafiya da fasfon kasashen Malawi ko Zambia. Umarnin ya bayyana cewa duk wanda "aka samu ya cancanci a ba shi nau’in visa na B1/B2 dole ne ya ajje $5,000, $10,000 ko $15,000, duba ga lokacin gana wa da mai neman visa din".
Yawancin matafiya da suka fito daga ƙasashen Malawi da Zambia - kuma ba kawai zuwa Amurka ba - sun firgita da matakin mahukuntan Amurka na daukar kowanne matafiyi daga kasashensu a matsayin wanda zai karya ka’idar visa.
Suna jin takaicin rashin fahimtar cewa ba kowane ɗan Malawi ko Zambiya ba ne da ke ziyartar Amurka don aiki, hutu ko ganin iyali da abokai ke da niyyar saba ka’idar visa ba.
Matemba ya nuna cewa "$15,000 kudi ne mai yawa har ma ga gwamnati da za ta kashe wa wani wanda zai ziyarci Amurka a matsayin wakilin kasarsa." Akwai ziyarar aiki da yawa da ke bukatar wakilcin gwamnatin Malawi, ciki har da babban taron Majalisar Dinkin Duniya.
Tsarin ya sauya kuidn neman visa na $185 zuwa wani adadi da kusan ba za a iya biya ba saboda yawan sa.
Karamin tikitin jirgi daga filin jirgin sama na Blantyre a Chileka zuwa filin jirgin sama na JFK da ke New York ya kai kusan dala 2,000 a halin yanzu, haka farashin yake daga filin jirgin sama na Kenneth Kaunda da ke birnin Lusaka na Zambia.
Hana cuwa-cuwa
Manazarta sun ce manufar ta yi daidai da dokar hana viza da aka kawa da sunan matakin samar da tsaro.
Majalisar Harkokin Musulunci ta Amurka (CAIR) ta yi tir da sabon matakin a matsayin nuna wariya, inda ta bayyana shi a matsayin wani nau'i na cin zarafi da kuma "halastacciyar shake wa".
"Wannan ba batun tsaron kasa ba ne," in ji Robert McCaw, dareaktan harkokin gwamnati na CAIR. "Yana shafi makamantar da manufofin gudun hijira da tatsar maziyarta, hukunta kasashen da ba a kauna, da mayar da shimfidar fuskar Amurka zuwa katangar biyan kudade makudai.”
Matakan sun farfado da wani mataki da aka fara gabatarwa a watan Nuwamban 2020, gaf da karshen wa'adin farko na Shugaba Donald Trump, amma ba a aiwatar da shi ba.
A cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, jami'an ofishin jakadancin kasar a duk duniya na da hurumin tantance adadin lamuni ga matafiya daga kasashen da ake zargin suna yawan karya sharuddan visa.
"Wannan matakin da aka yi shi da gayya, na ƙarfafa himmar gwamnati ga dokar shige da fice ta Amurka tare da hana wuce gona da iri wajen zama," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Tammy Bruce.
Sabbin ka’idojin na ƙara wani nau'i na rikitar da lamarin neman visar zuwa Amurka.
Dole ne masu dauke da visa waɗanda suka biya kudaden na lamuni su zo su fita daga Amurka ta tashoshin shiga guda uku: Filin jirgin saman Boston Logan, Filin Jirgin Sama na JFK da Filin jirgin saman Washington Dulles.
Matafiya da suka zo ko suka tashi daga wani filin jirgin, na iya fuskantar hukuncin hana su shiga ko kuma yanayin ba a yi musu rajista daidai ba.
Za a mayar wa da matafiya kudin da suka biya idan suka bar Amurka a lokacin da kwanakin da aka amince su zauna suka zo karshe, suka kuma cika dukkan sharuddan visa. Har yanzu dai ba wani aba da ya inganta.
Kiran ba zata
Wasu na ganin wata babbar dama a cikin wannan babban mataki da Amurka ta dauka.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya rawaito Anthony Mukwita tsohon jakadan kasar Zambia na fadin cewa, maimakon mafarkin wada, manufar wani yunkuri ne na ganin nahiyar Afirka ta zama abin sha'awa ga 'yan nahiyar.
"Zambia kasa ce mai arzikin albarkatun kasa," in ji shi. "Muna da murabba'in kilomita 750,000, wanda kashi 90 cikin 100 na wannan fili kasar noma ce, za mu iya noma, za mu iya samar da abinci mai yawa, za mu iya rage talauci, kuma 'yan Zambia za su zauna a Zambia maimakon yin layi suna neman vizar dala 15,000."
Tare da ɗimbin ma'adanai, shimfidaddiyar kasa mai kyan gani da kyawawan al'adu da suka bazu a cikin nahiyar, Matemba ya yarda cewa lokaci ya yi da za a nuna Afirka a matsayin wurin da ya cancanci ziyarta kamar ko'ina a duniya.
"Wannan darasi ne ga yawancin kasashen Afirka kan yadda za mu tsara kanmu a matakin kasa da kasa, da kuma jin dadin cewa kasashe na iya canzawa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Kiran bayar da hujja
Matemba na fatan gwamnatocin Malawi da na Zambia za su iya shawo kan hukumomin Amurka da su yi la'akari da masu neman viza duba ga daidaikun mutane maimakon aiwatar da wannan sabuwar manufar a matsayin wani mataki na dakile zargin karya ka’idar zama da sharadin visa.
"Kakaba wa kowa laifi zai zama rashin adalci… Yawancin su suna zuwa Amurka don kasuwanci ko aikin likita kuma su dawo," in ji shi. "Abin ban mamaki shi ne cewa muna daɗa haɗe wa a matsayin duniya daya da take kamar wani kauye guda, amma duk da haka waɗannan tsare-tsaren vizar suna hana mutane damar musayar kwarewa, al'adu, al'amuran zamantakewa da tattalin arziki har ma da sababbin abubuwa."
Trump dai ya dauki mataki mai tsauri kan bakin haure tun bayan komawar sa kan karagar mulki a watan Janairu a karo na biyu. Ya fitar da dokar hana shiga Amurka a watan Yuni wadda ke hana 'yan kasashe 19 gaba daya ko kuma wani bangare shiga Amurka bisa dalilan tsaron kasa.
Sanarwar da aka fitar a rajistar bayanan tarayya ta nuna cewa "ana iya amfani da bayanan da aka tattara a lokacin binciken, don sanin tasirin lamunin viza wajen rage yawan karya ka’idar zama, duba damuwar da ake da ita game da rashin yin tantancewar da ta kamata”.
Har zuwa lokacin da za a kammala wannan nazari, tafiya zuwa Amurka zai haifar da sauye-sauye masu yawa ga ƙwararru kamar Matemba - waɗanda ba za su manta da gida ba ballantana su zauna da karya ka’ida a kasashen waje.