Rundunar ‘yan sandan Ghana ta kama wasu mutum biyu da aka gani a wani bidiyo na TikTok suna barazanar cutar da Shugaban Ƙasar John Dramani Mahama da uwargidansa Lordina Mahama.
A cewar hukumar ‘yan sandan, wasu mutanen da ake zaton suna da hannu a cikin batun sun arce, amma ana ci gaba da farautar su domin gudanar da bincike a kansu.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a ranar 12 ga watan Agustan 2025, ta ce “hukumar ‘yan sandan Ghana ta fara gudanar da bincike kan wani bidiyo na TikTok wanda a cikinsa aka ji wani mutum yana barazana ga rayuwar Shugaban Ƙasar, John Dramani Mahama da kuma mai ɗakinsa Lordina Mahama.
"Zuwa yanzu, mutane biyu, Prince Ofori da Yayra Abiwu, suna hannun 'yan sanda kana suna taimaka wa wajen binciken da ake yi, yayin da ake kokarin ganin an samu wasu mutanen da ake kyautata zaton suna da alaƙa da bidiyon don taimakawa wajen gudanar da bincike."