Ofishin Shugaban Ƙasar Ghana ya ba da umarni ga shugabannin addini su dinga miƙa ‘saƙonnin ikirarin wahayi masu muhimmanci ga ƙasa’ domin a tantance su a hukumance.
An ɗauki matakin ne domin aiki kan gargaɗi na ruhi mai alaƙa da manyan shugabanni da aikin gwamnati da tsaron ƙasa da kuma zaman lafiyar al’umma, in ji wata sanarwa daga ofishin kula da addinai na fadar shugaban ƙasar, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito ranar Lahadi.
Umarnin yana zuwa ne bayan wani hoton bidiyo ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta inda wasu limaman Kiristoci ke iƙirarin cewa sun ga hatsarin helikwaftan da ya kashe jami’an gwamnatin kafin ya auku.
Hatsarin helikwaftan ya auku ne ranar 6 ga watan Agusta na shekarar 2025, a lokacin da wani jirgin soji mai ɗauke da jami’an gwamnati ya faɗi, lamarin da ya sa jami’an gwamnati bakwai suka rasa rayukansu.
Jana’izar waɗanda lamarin ya shafa
Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da Ministan Tsaro Edward Omane Boamah da Ibrahim Murtala Mohammed, tsohon ministan muhalli da kimiyya da fasaha.
Hasarin ya janyo tashin hankali a fadin ƙasar lamarin da ya sa aka yi ta juyayi da ta’aziyyya.
An riga na yi jana’izar waɗanda lamarin ya rutsa da su inda aka yi jana’izar Minista Ibrahim Murtala Muhammed da kuma Mataimakin Sakataren da ke jagorancin harkar tsaro ta ƙasa Limuna Muniru Mohammed ranar Lahadi, 10 ga watan Agusta.
An sa ranar jana’izar sauran mamatan ciki har da Edward Omane Boamah ranar 15 ga watan Agusta.
Yayin da Ghana ke jimamin rasa waɗannan manyan mutanen, matakin da gwamnatin ta ɗauka na aiki da shugabannin addini game da ‘saƙonnin wahayi’ ya nuna wani mataki domin sanin yadda za ta yi da lamari mai hargitsi tsakanin addini da aikin gwamnati da kuma zamantakewa a ƙasar.