Wata kotu a Chadi ta yanke wa shugaban ‘yan adawa kuma tsohon Firaminista Succes Masra hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan ta same shi da laifin tayar da rikicin ƙabilanci wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40 a kudu maso yammacin ƙasar a watan Mayu.
Wata kotu ta musamman a babban birnin Chadi, N'djamena, ta same shi da laifin furta kalaman ƙiyayya da nuna ƙiyayya ga baƙi da kuma tunzura jama’a domin aikata kisan-kiyashi, in ji Francis Kadjilembaye, ɗaya daga cikin lauyoyin kare shi, yayin da yake magana da manema labarai ranar Asabar.
Kotun ta kuma umarci Masra da ya biya tara ta CFA biliyan 1, kimanin dala miliyan 1.8
Masra ya musanta zarge-zarge yayin shari'ar
Lauyoyinsa sun yi iƙirarin cewa masu gabatar da kara sun kasa gabatar da hujjojin da suka tabbatar da hannunsa a cikin lamarin.
A makon da ya gabata, masu gabatar da kara sun nemi kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 25 a gidan yari.
An yi shari'ar Masra tare da wasu mutane 74 da ake zargi da hannu a aikata kisan-kiyashi.
Masra, wanda shi ne shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Chadi, Les Transformateurs (Transformers), an kama shi a ranar 16 ga Mayu bayan rikicin kabilanci a lardin Logone Occidental wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 42 a ranar 14 ga Mayu.
Ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2024
A watan Yuli, ya shiga yajin cin abinci don nuna rashin jin daɗinsa kan tsare shi. Ya daina yajin cin abincin bayan kusan mako guda, bayan wata zanga-zangar mata da suka nemi a sako shi.
Masra ya tsaya takarar shugaban kasa a zaɓen watan Mayu 2024, wanda tsohon shugaban rikon ƙwarya Mahamat Idriss Deby ya lashe.