Ƙwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fara muhawara a ranar Litinin kan wani ƙuduri da Faransa ta tsara na tsawaita wa'adin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a kudancin Lebanon na tsawon shekara guda da nufin janyewa.
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila da Amurka na adawa kan sabunta wa’adin rundunar, kuma babu tabbas ko daftarin zai samu goyon bayan Washington, wadda ke da ƙarfin iko a majalisar.
Wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce "ba mu ce komai kan tattaunawar da kwamitin sulhu na MDD ke yi ba," yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar dakarun MDD da ke Lebanon (UNIFIL), waɗanda aka tura tun shekarar 1978 don sa ido kan janyewar sojojin Isra'ila bayan sun mamaye Lebanon, da kuma taimaka wa gwamnatin Lebanon wajen mayar da iko a kan iyakar yankin.
Batun, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fara wallafawa, zai “ƙara wa’adin UNFIL har zuwa 31 ga Agustan 2026,” sai dai yana nuna aniyarsa ta yin aiki kan janyewar UNIFIL."
Hakan zai kbiyo da sharadin cewa gwamnatin Lebanon ce ita kadai" ke samar da tsaro a kudancin Lebanon... da kuma cewa bangarorin sun amince da wani tsari na siyasa."
Ƙarkashin wata yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen yakin baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da Hezbollah wadda ke samun goyon bayan Iran, an ci gaba da jibge sojoji a Beirut da kudancin Lebanon tare da wargaza ababen more rayuwa na ƙungiyar a can.
Isra'ila ta ci gaba da kai hari a Lebanon
Kasar Labanon dai na fama da ƙalubalen batun wargaza ƙungiyar Hizbullah, inda ko a cikin wannan wata sai da majalisar zartaswar ƙasar ta ɗora wa sojojin ƙasar alhakin aikin samar da wani shiri da zai yi hakan a zuwa ƙarshen shekara.
Ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran ta ja baya.
Ƙarkashin yarjejeniyar dai, an so Isra'ila ta fice daga ƙasar ta Lebanon gaba ɗaya, duk da cewa ta jibge dakarunta a yankuna da dama da take ganin suna da muhimmanci kuma tana ci gaba da kai hare-hare a faɗin ƙasar ta Lebanon.
Kazalika sojojin na Isra'ila sun yi ta arangama da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Daftarin kudurin da ake kan tattaunawa akai ya kuma yi ƙira da a inganta koƙarin diflomasiyya don warware duk wata taƙaddama da ta shafi iyakar ƙasa da ƙasa tsakanin Lebanon da Isra'ila.
Mambobin majalisar dai na muhawara ne kan daftarin kudurin da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya gani a ranar Litinin gabanin kuri'ar da mambobi 15 za su kada a ranar 25 ga watan Agusta kafin cikar wa'aɗin rundunar a ƙarshen wata.