GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Jamus ta dakatar da fitar da kayayyakin soji zuwa Isra'ila har sai abin da hali ya yi
Shugaban Gwamnatin Jamus, Merz ya zargi shirin Isra'ila na mamaye Gaza, yana cewa ba zai ba da izinin sake fitar da duk wasu kayayyakin soji ba zuwa Isra'ila ba a wannan yaƙin da take yi da Gaza a wannan gaɓar.
Jamus ta dakatar da fitar da kayayyakin soji zuwa Isra'ila har sai abin da hali ya yi
Jamus ta ce dakatar da yaƙi a Gaza shi ne abin da take fifitawa. / Reuters
8 Agusta 2025

Gwamnatin Jamus ta yi suka mai tsanani kan shirin Isra'ila na mamaye Gaza, tare da sanar da dakatar da wani ɓangare na fitar da kayayyakin soji zuwa Isra’ila har sai abin da hali ya yi.

“A cikin irin wannan yanayi, gwamnatin Jamus ba za ta amince da fitar da kayan soji da za a iya amfani da su a Gaza ba,” in ji Firaminista Friedrich Merz a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

Shugaban mai ra’ayin mazan jiya ya bayyana cewa Jamus ta kasance tana kare hakkin Isra’ila na kare kanta, tana goyon bayan matakan sakin wadanda aka yi garkuwa da su, da kuma kokarin hana Hamas makamai, tare da goyon bayan Isra’ila a duk lokacin rikicin.

“Shawarar Majalisar Ministocin Isra’ila da aka yanke a daren jiya na ci gaba da daukar matakan soji masu tsanani a Gaza na kara wahalar ganin yadda za a cim ma wadannan manufofi daga hangen gwamnatin Jamus,” in ji Merz, yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta ƙara amincewa da fitar da kayan soji zuwa Isra’ila da za a iya amfani da su a wannan yaƙin ba.

Matsalar jinƙai mai tsanani

Firaministan ya kuma bayyana damuwar Berlin kan matsalar jinƙai mai tsanani da ke faruwa a Gaza, inda rahotanni suka nuna cewa yara na mutuwa saboda yunwa da kuma karancin abinci da ke addabar al’ummar Falasdinawa sakamakon takunkuman Isra’ila da hare-haren soji.

“Gwamnatin Jamus na matukar damuwa kan ci gaba da wahalar da al’ummar farar hula a Gaza. Tare da wannan shirin kai farmaki, gwamnatin Isra’ila za ta dauki nauyin da ya fi na baya,” in ji Merz, yana mai jaddada kiran da ya yi ga Isra’ila da ta ba da damar kai dauki ga kungiyoyin agaji, ciki har da na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin fararen hula.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Isra’ila “da kada ta dauki wani mataki na ƙara mamaye Yammacin Kogin Jordan,” a yayin da damuwar duniya ke ƙaruwa cewa irin wadannan matakai na iya ƙara dagula al’amura da kuma kawo cikas ga damar samun mafita ta ƙasashe biyu.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us