Isra'ila ta kashe 'yan jarida biyu na Aljazeera a harin da ta kai wani tantin 'yan jarida kusa da asibitin Al-Shifa da ke yammacin birnin Gaza.
Tashar talabijin ta Qatar ta ambato daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa a Gaza, wanda ya ce, "Ma'aikatan gidan talabijin na Al Jazeera Anas al-Sharif da Mohamed Qraiqea, sun yi shahada a wani harin da Isra'ila ta kai kan tantinsu."
Kazalika Aljazeera ta kuma tabbatar a ranar Lahadi cewa, harin ya kashe wasu masu ɗaukar hoto na kafar guda biyu, Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal.
"An kashe ɗan jaridar Al Jazeera na sashen Larabci Anas Al-Sharif da Mohammed Qreikeh a wani harin da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza, tare da masu ɗaukar hoto Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal," kamar yadda kafar ta bayyana.
A ɓangare guda, ita ma Isra'ila ta tabbatar da cewa ta kashe ɗan jaridan, inda ta yi iƙirarin cewa shi ne shugaban ƙungiyar Hamas.
Sa’o’i kaɗan kafin a kashe shi, al-Shariff, wanda ya kasance mai ba da rahoto kan kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza, ya ba da labarin harin da ya yi sanadiyar ɗaukar ransa.
"An yi ta kai harin bama-bamai ba ƙaukautawa ...har tsawon sa'o'i biyu, hare-haren Isra'ila sun tsananta a birnin Gaza," kamar yadda al-Sharif ya bayyana a shafinsa na X.
Jim kaɗan, wasu 'yan jarida suka fitar da sanarwar mutuwarsa, kafin Al Jazeera ta tabbatar da hakan.
Sakon ƙarshe na l-Sharif
Bayan rasuwarsa ne masu kula da shafinsa na X suka wallafa wasiyyarsa, inda ya roki Allah da ya ƙarbe shi daga cikin shahidai, kuma ya gafarta masa zunubansa.
"Fatana shi ne Allah ya tsawaita rayuwata har sai na koma wurin iyalina da masoyana a garinmu na asali, Ascalon da aka mamaye, 'Majdal.’ Allah ya ƙaddara hakan cikin ikonsa kuma hukuncinsa ya cika,” in ji al-Sharif a cikin wasiyyarsa.
"Na yi rayuwa cikin ƙunci kuma na ɗanɗana asara da baƙin ciki a lokuta da dama. Amma duk da haka, ban yi ƙasa a gwiwa ba ko na kwana ɗaya don isar da gaskiya a yadda take, ba tare da murɗiya ko faɗar ƙarya ba, ina fatan Allah ya yi hisabi ga waɗanda suka yi shiru, da waɗanda suka amince a kashe mu, da waɗanda suka hana mu numfashi, suka ƙi jin tausayin 'ya'yanmu da matanmu."
A wasiyyarsa, ya bai wa al’ummar Larabawa da Musulman duniya amanar Falasɗinu da al’ummarta, ya kuma buƙace su da ka da su yi shiru, su zama wata gada ta ‘yantar da Falasɗinawa.
Ya kuma bai wa duniya amanar iyalansa da suka haɗa da mahaifiyarsa da matarsa da ɗansa da kuma 'yarsa.
‘‘Ka da ku manta da Gaza…kuma ka da ku manta da ni a cikin addu’o’inku, ku roƙa min yafiya da samun karɓuwa, ‘‘ in ji al-Sharif.
Harin da ya kashe al-Sharif ya kashe wasu mutane shida, biyar daga cikinsu 'yan jarida ne.
Kisan ‘yan jaridun biyar, ya sa jimillar ‘yan jaridan da Isra’ila ta yi wa kisan killa a Gaza tun daga karshen shekarar 2023 ya kai 237.