Majalisar zartarwar Sudan ta yi zamanta na farko ranar Talata a babban birnin ƙasar Khartoum wanda rabon da aka yi rinsa tun bayan da yaƙi ya ɓarke da rundunar (RSF) a watan Afrilun shekarar 2023.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar SUNA ya bayyana zaman, wanda Firaminista Kamal Idris ya jagoranta, a matsayin “wani mataki na mayar da hukumomin gwamnati babban birnin ƙasar, yayin da ake shirye-shiryen samar da tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.”
Gabanin zaman na ranar Talata, gwamnatin Sudan ta tana gudanar da lamuran mulkin ƙasar ne daga fadar gwamnati ta wucin-gadi a Port Sudan da ke gabashin ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran SUNA ya ruwaito cewa zaman ya tattauna shirye-shiryen dukkan ma’aikatan Sudan na wannan shekarar, inda ya mayar da hankali kan yi wa jama’a hidima da tsaro da sake gina ƙasar da kuma tabbatar da bai wa mutane damar komawa gidajensu bisa raɗin kansu.
Ranar 31 ga watan Mayu ne dai aka rantsar da Idris a matsayin sabon Firaminista a gaban shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya Abdel Fattah al-Burhan.
Tun da yaƙin ya ɓarke, Khartoum ya kasance fagen yaƙi tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF, wadda ta yi iko da yawancin wurare a babban birnin ƙasar ban da hedkwatar soji da kuma wasu wuraren soji a Khartoum da Bahri da kuma Omdurman.
A cikin ‘yan watannin nan, wuraren da RSF ta yi iko da su sun ragu cikin sauri a faɗin ƙasar Sudan inda sojin ƙasar take ƙwace su, kuma rundunar sojin ta faɗaɗa nasararta kan wurare da suka haɗa da jihohin Khartoum da White Nile.
Ranar 21 ga watan Mayu 21, rundunar sojin Sudan ta yi shelar cewa ta sake karɓe cikakken iko da Khartoum, inda ta ayyana babban birnin ƙasar a matsayin birnin da ya tsira daga dakarun RSF.
Rikicin ya kashe sama da mutum 20,000 tare da raba mutum miliyan 15 da gidajensu, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin cikin gida, yayin da wani hasashe na jami’’o’in Amurka ya kiyasta cewa mutanen da suka mutu a yaƙin sun kai 130,000.