Shugaban ƙasar Ghana John Mahama ya dakatar da harkokinsa tare da ayyana makoki na kwanaki uku a faɗin ƙasar sakamakon hatsarin jirgin helikwafta na soji wanda ya kashe manyan jami’an gwamnatinsa a ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ambato wata sanarwa daga ministan watsa labarai kuma mai magana da yawun gwamnati, Mista Felix Kwakye Ofosu, tana cewa shugaban ya ɗauki matakin nan-take domin martaba waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙasar za ta yi juyayin kwanaki uku daga ranar Alhamis, 7 ga watan Agustan shekarar 2025.
Mista Julius Debra, shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasar, ya ba da umarnin cewa a yi ƙasa-ƙasa da tutocin ƙasar.
Hatsarin na jirgi mai saukar ungulu na sojin ƙasar Ghana ya faru ne da safiyar Laraba a Adansi-Akrofuom a lardin Ashanti na ƙasar.
Waɗanda suka rasu a hatsarin sun haɗa da Dakta Edward Kofi Omane Boamah, Ministan Tsaro, da Dakta Ibrahim Murtala Mohammed, Ministan Muhalli da Kimiyya da Fasaha, da Alhaji Muniru Mohammed, muƙaddashin mataimakin shugaban gudanarwar harkar tsaro, da Dakta Samuel Sarpong, mataimakin shugaban Jam’iyyar NDC, da kuma Mista Samuel Aboagye, tsohon ɗan takarar majalisar dokoki.
Sauran waɗanda suka rasu sun haɗa da Peter Bafemi Anala (matuƙin jirgi) da Manaen Twum Ampadu (matuƙin jirgi) da kuma sajent Ernest Addo Mensah.
Tawagar dai tana kan hanyarta ta zuwa Obuasi ne domin halartar bikin ƙaddamar da shirin inganta yadda ake haƙar ma’adinai ga ƙananan masu haƙar ma’adinai.