AFIRKA
1 minti karatu
Tiani ya kafa sabuwar hukumar sa ido kan kafafen yaɗa labarai ta Nijar
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP ya rawaito cewa Shugaban Ƙasar ya naɗa ɗan jarida, Ibrahim Gambo Diallo a matsayin shugaban hukumar ta ONC.
Tiani ya kafa sabuwar hukumar sa ido kan kafafen yaɗa labarai ta Nijar
Shugaban ƙasar Nijar Janar Tiani ya kafa sabuwar hukumar ne tare da sabon shugabanta. / RTN
12 awanni baya

Shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani ya rattaɓa hannu kan dokar da ta kafa hukumar sa ido kan kafafem yaɗa labarai ta ƙasar (ONC).

Hukumar ta ONC za ta yi aiki ne domin kare ‘yancin ‘yan jarida da kuma kafafen yaɗa labarai tare da bai wa kowa ikon amfani da kafafen yaɗa labarai da kuma tabbatar da cewa kafafen na biyayya ga ɗa’ar aikin jarida a ƙasar Nijar, In ji kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP.

Jim kadan bayan sanar da kafa sabuwar hukumar e kuma, sai Shugaba Tiani ya naɗa wani ƙwararren ɗan jarida Ibrahim Manzo Diallo a matsayin shugaban hukumar ta ONC.

Kazalika hukumar na da alhaƙin kare a’adu musamman tallata yarukan ƙasa a kafafen yada labarai domin tabbatar da cewa ana mutunta ɗabi’u da al’adu masu kyau a kafafen yaɗa labaran.

Har wa yau hukumar ta za ta rinƙa bai wa gwamnatin ƙasar shawarwari da suke da alaƙa da aikin jarida.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP ya ruwaito cewa shugaban ƙasar ya naɗa ɗan jarida, Ibrahim Gambo Diallo, a matsayin shugaban hukumar ta ONC.

Ɗan jaridar yana da alaƙa da kafafen yaɗa labarai da dama ciki har da Aïr Info ta tashar Damagaram da kuma ta Sahara FM.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us