Wata mummunar zaftarewar ƙasa ta shafe wani ƙauye a yankin Darfur na Yammacin Sudan, inda ta kashe mutane aƙalla 1,000 a ɗaya daga cikin mafi munin iftila’in yanayi da ƙasar da ke yakin Afirka ta taɓa fuskanta a baya bayan nan, kamar yadda wata ƙungiyar ‘yan tawaye da ke riƙe da iko da yankin ta bayyana a yammacin ranar Litinin.
Lamarin dai ya afku ne a ranar Lahadi a ƙauyen Tarasin da ke tsaunukan Marrah na tsakiyar Darfur, bayan da aka shafe kwanaki ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙarshen watan Agusta, in ji wata sanarwa da ƙungiyar Liberation Moverment-Army ta Sudan ta fitar.
"Bayanan farko da aka samu sun bayyana cewa dukkan mazauna ƙauyen sun mutu, waɗanda aka ƙiyasta sun fi mutum dubu ɗaya,” a cewar sanarwar.
Ƙauyen ya shafe gaba ɗaya, in ji ƙungiyar, inda ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da su taimaka wajen gano gawarwakin.
Bala'i a cikin yaki
Gwamna Minni Minnawi da ke da kusanci da sojojin Darfur, ya bayyana zaftarewar ƙasar a matsayin "mummunan bala'i da ya wuce iyakokin yankin".
“Muna kira ga ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da su gaggauta kawo ɗauki tare da bayar da tallafi a wannan mawuyacin lokaci, domin bala’in ya fi abin da mutanenmu za su iya jurewa su kaɗai,” in ji shi a cikin wata sanarwa.
Yawancin lardunan yankin Darfur, ciki har da yankin da aka samu zaftarewar ƙasa, ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ba sa iya shiga sakamakon yaƙin da ake ci gaba da gwabzawa, wanda ya yi matuƙar taƙaita isar da agajin jinƙai da ake buƙata cikin gaggawa.
Kazalika, iftila’in dai ya zo ne a daidai lokacin da Sudan ke ci gaba da fama da yaƙin basasa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF, wanda ya fara tun a watan Afrilun 2023, inda ya kashe dubun-dubatar mutane tare da haifar da matsalar jinƙai mafi girma a duniya.
Haka kuma tun a bara ƙasar ke fama da ɓullar cutar kwalara, wadda ta kashe fiye da mutane 2,500, a cewar hukumomin lafiya.