Hamas ta yi maraba da kuri'ar da MDD za ta kada kan tsagaita wuta a Gaza
Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar Hamas ta tabbatar da mayar da martani mai kyau ga duk wani kudiri da zai kai ga tsagaita wuta.
Hamas ta yi maraba da kuri'ar da MDD za ta kada kan tsagaita wuta a Gaza
Hamas ta yi maraba da kokarin MDD na ganin an tsagaita wuta a Gaza. / AA
12 Disamba 2024


Kungiyar Hamas ta yi marhabin da kudurin Majalisar Dinkin Duniya na neman tsagaita wuta a Gaza tare da yin kira ga kasashen duniya da su tilasta wa Isra'ila aiwatar da shi.

Kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar a Telegram ta ce, "Muna maraba da zartar da gagarumin kuduri da babban taron MDD ya yi, na neman tsagaita wuta a Gaza.

“Da kuma bai wa fararen hula damar samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum da jinkai cikin gaggawa da ba su agaji, da kuma kin amincewa da duk wani yunkuri na kashe Falasdinawa da yunwa."

Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar Hamas ta tabbatar da mayar da martani mai kyau ga duk wani kudiri da zai kai ga tsagaita wuta.

Ta jaddada cewa Netanyahu da "ministocinsa na 'yan ta'adda" suna watsi da laifin yaƙin da ake tuhumarsu da shi da kuma duk wani kokari na kawo karshen kazamin yakinsu na kisan kare dangi kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us