GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Isra'ila na tattaunawa da ƙasashe da dama domin tursasa kai musu Falasɗinawan Gaza
Tashar Channel 12 ta Isra'ila ta ruwaito cewa ƙasar na tattaunawa da Indonesia da Somaliland da Libiya da Sudan ta Kudu, sai dai daga baya Sudan ta Kudu ta musanta tattaunawa wani abu makamancin haka da Isra'ila.
Isra'ila na tattaunawa da ƙasashe da dama domin tursasa kai musu Falasɗinawan Gaza
Wannan na zuwa ne a lokacin da Isra'ila ke fuskantar shari'ar kisan ƙare-dangi a Kotun Duniya ta Shari'a saboda yaƙin da take yi a wannan yanki. / AA
14 Agusta 2025

Isra'ila tana tattaunawa da ƙasashe hudu da yankin Somaliland wanda ya ɓalle daga Somaliya, domin bincika yiwuwar tilasta kwashe Falasɗinawa daga Gaza, kamar yadda kafafen yada labarai na Isra'ila suka bayyana a ranar Alhamis. Wannan mataki ya fuskanci suka sosai a matsayin take hakkin dokokin ƙasa da ƙasa.

Tashar Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito cewa an samu "ci gaba" a tattaunawa da Indonesia da Somaliland, wanda ya ɓalle daga Somaliya sannan ya ayyana 'yancin kai a shekarar 1991 amma ba a amince da shi ba a hukumance.

Kafar ta bayyana sunayen Indonesia, Libya, Uganda, Sudan ta Kudu, da Somaliland a matsayin bangarorin da ke cikin tattaunawar.

Ta ambaci wata majiyar Isra'ila da ba a bayyana sunanta ba, wadda ta ce wasu ƙasashe sun nuna "alamun ƙofarsu a buɗe take" wajen karbar Falasdinawan da aka tilasta musu barin gidajensu saboda yakin Gaza, duk da cewa ba a cimma wata yarjejeniya ba tukuna.

A safiyar Alhamis, Sudan ta Kudu ce kadai ta mayar da martani a hukumance, inda ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar da wata sanarwa a ranar Laraba tana ƙaryata rahotannin da ke cewa tana tattaunawa da Isra'ila, tana mai kiran su "marasa tushe" kuma ba su dace da manufofin ƙasar ba.

Kafafen yada labarai na Isra'ila sun kuma ruwaito cewa Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Sharren Haskel, ta isa Sudan ta Kudu a ranar Laraba, a ziyarar farko da wani jami'in Isra'ila ya kai ƙasar, tare da hasashen cewa tafiyarta na da alaƙa da shirin kwashe Falasɗinawan.

Shirye-shiryen tilasta kwashe Falasdinawa daga Gaza sun fuskanci ƙin amincewa daga Falasdinawa, ƙasashen Larabawa, da kuma mafi yawan al'ummar duniya, suna masu bayyana shi a matsayin take dokokin jin kai da haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa.

Sojojin Isra'ila, suna yi watsi da kiraye-kirayen duniya na tsagaita wuta, sun ci gaba da kai farmaki mai tsanani a Gaza tun watan Oktoba 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa fiye da 61,700.

A watan Nuwamban da ya gabata, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta fitar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant bisa zargin aikata manyan laifuka da kuma laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza.

Isra'ila tana kuma fuskantar shari'ar kisan ƙare-dangi a Kotun Duniya ta Shari'a saboda yaƙin da take yi a wannan yanki.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us