Ƙasashen Turkiyya da Sifaniya da Birtaniya da kuma Jamus sun yi Allah wadai da amincewar da Isra’ila ta yi ta samar da sabbin matsugunai ba bisa ka’ida ba a yankin E1 wato Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, suna masu gargaɗin cewa hakan zai kawo cikas ga tsarin samar da ƙasashe biyu da kuma keta dokoƙin ƙasa da ƙasa.
A ranar Alhamis, kafofin yaɗa labaran Isra'ila suka ba da rahoton cewa Ministan Kuɗi na ƙasar Bezalel Smotrich ya amince da gina matsugunan mutane 3,401 a Ma'ale Adumim da ke Gabashin Birnin Ƙudus, da kuma wasu 3,515 a yankunan da ke kewaye.
Aikin dai na da nufin raba Yammacin Kogin Jordan zuwa arewaci da kudancin ƙasar, tare da mayar da Gabashin Birnin Ƙudus saniyar ware.
Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce matakin ya yi watsi da dokoƙin ƙasa da ƙasa da kuma ƙudurorin Majalisar Ɗinkin Duniya sannan hakan "na nufin take ‘yancin samar da ƙasar Falasɗinu, da manufar samar da ƙasashe biyu, da kuma fatan da ake da shi na samun zaman lafiya mai ɗorewa."
Kazalika, ma’aikatar ta sake jadadda goyon bayan Turkiyya ga ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta bisa kuɗurin yarjejeniyar iyakoki na 1967 da kuma Gabashin Ƙudus a matsayin babban birninta.
Ministan Harkokin Wajen Sipaniya Jose Manuel Albares ya kira faɗaɗa yankin da wani "sabon saba dokokin ƙasa da ƙasa" wanda "ya gurgunta yiwuwar samar da zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu wanda ke zama hanya daya tilo ta zaman lafiya," tare da yin Allah wadai kan tashe-tashen hankula na raba matsugunai.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy, ya ce ‘‘halin da ake ciki a Gaza yana ƙara ta'azzara sakamakon ayyukan Isra'ila, wanda ke ƙara yin barazana ga tsarin samar da ƙasashe biyun.’’
Ya ce ya tattauna da takwarorinsa na Canada da Faransa kan buƙatar tsagaita buɗe wuta cikin gaggawa, da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma kara kai agajin jinƙai.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bukaci Isra'ila da ta "dakatar da gine-ginen" kana ta ce "ta yi watsi da" shirin ƙara dubban sabbin gidaje a yammacin kogin Jordan da ta mamaye.
Kazalika Ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta yi Allah-wadai da matakin a matsayin wani bangare na ra'ayin Firaiminista Benjamin Netanyahu na shirin samar da "Greater Israel’', yana mai gargadin cewa za ta ƙarfafa mamayar da kuma kawar da fatan samun ƙasar Falasɗinu.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauki matsugunan da Isra'ila ke shirin yi a yammacin gaɓar kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus a matsayin take doka karkashin dokoƙin ƙasa da ƙasa.
A watan Yuli ne, kotun ƙasa da ƙasa ta ayyana mamayar da Isra'ila ke yi a yankin Falasdinu a matsayin haramtacce tare da yin ƙira da a kwashe dukkan matsugunan.
Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun sha yin gargaɗin cewa ci gaba da faɗaɗa matsugunan na barazana ga yiwuwar samar da maslaha tsakanin ƙasashe biyu - tsarin da ake kallo a matsayin mabuɗi ko hanyar kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Falasɗinu da aka kwashe shekaru ana yi.