Gwamnatin Sudan ta Kudu ta musanta rahotannin da ke cewa ta shiga tattaunawa da Isra'ila don mayar da Falasɗinawa daga Gaza zuwa can, tana mai cewa ta “ƙaryata ƙwarai” iƙirarin da aka yi kwanan nan a kafofin watsa labarai na Isra'ila, da ke nuna wannan shirin.
Sudan ta Kudu “ta ƙaryata ƙwarai rahotannin kafofin watsa labarai na kwanan nan da ke cewa Gwamnatin Jamhuriyar Sudan ta Kudu tana tattaunawa da Jamhuriyar Isra'ila kan zaunar da 'yan ƙasar Falasɗinu daga Gaza zuwa Sudan ta Kudu,” in ji wata sanarwa daga Ma'aikatar Harkokin Wajen ƙasar a ranar Laraba.
Ma'aikatar ta bayyana cewa waɗannan iƙirari “ba su da tushe kuma ba su wakiltar matsayi ko manufofin hukumar” gwamnatin Sudan ta Kudu.
Gwamnatin ta yi kira ga kafofin watsa labarai da su “yi taka-tsan-tsan” tare da tabbatar da sahihancin labarai daga majiyoyin hukuma kafin wallafa su.
Tagayyara Falasɗinawa
Kafofin watsa labarai na Isra'ila sun ruwaito cewa Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Sharren Haskel, ta isa Sudan ta Kudu a safiyar ranar Laraba, a ziyarar farko ta hukuma da jami'in gwamnatin Isra'ila ya kai ƙasar.
Jaridar Times of Israel ta ambaton majiyoyi, tana cewa ziyarar ta nufi tattauna shirin Isra'ila na zaunar da al'ummar Falasdinu daga Gaza zuwa Sudan ta Kudu.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta bayyana cewa gwamnatin Tel Aviv tana tattaunawa da ƙasashe biyar, ciki har da Sudan ta Kudu, kan tsugunar da Falasɗinawa a yankunansu.
A Fabrairu, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Washington za ta “karɓi Gaza” tare da zaunar da Falasɗinawa a wani wuri daban a ƙarƙashin wani shiri na sake gina yankin, inda ya ce zai iya mayar da Gaza ta zama “Riviera ta Gabas ta Tsakiya.”
An yi tir da shirin Trump
Wannan shiri ya samu Allah-wadai daga Falasɗinawa, da ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashe da dama a duniya, ciki har da Canada, Faransa, Jamus, da Birtaniya.
Sojojin Isra'ila sun ƙaddamar da mummunan farmaki kan Gaza tun watan Oktoba 2023, inda suka kashe sama da Falasɗinawa 61,700, yawancinsu mata da yara.
A Nuwamban da ya gabata kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta fitar da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant saboda laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza.
Isra'ila tana fuskantar shari'ar kisan ƙare-dangi a Kotun Duniya ta ICJ, saboda yaƙin da take yi a wannan yankin.