DUNIYA
1 minti karatu
Turkiyya ta miƙa saƙon ta'aziyya ga Pakistan kan mutuwar ɗaruruwan 'yan ƙasar a ambaliyar ruwa
Turkiyya ta miƙa saƙon ta'aziyya ga ƙasar Pakistan kan mutuwar 'yan ƙasar sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a yankuna daban-daban na ƙasar.
Turkiyya ta miƙa saƙon ta'aziyya ga Pakistan kan mutuwar ɗaruruwan 'yan ƙasar a ambaliyar ruwa
Galibin waɗanda lamarin ya shafa sun fito ne daga yankin Khyber Pakhtunkhwa mai cike da tsaunuka, a cewar Hukumar Kare Aukuwar Bala'i ta ƙasar. / AA
19 awanni baya

Turkiyya ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga ƙasar Pakistan ranar Asabar sakamakon mutuwar ɗaruruwan ‘yan ƙasar a ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar.

"Muna matuƙar baƙin ciki game da rasa rayukan da aka yi sakamakon ambaliyar ruwa a Pakistan," a cewar wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

Ta ƙara da cewa: "Muna addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma muna miƙa ta’aziyyarmu ga Pakistan."

Hukumomi a Pakistan ranar Asabar sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya zarta 321.

Galibin waɗanda suka mutu sun fito ne daga lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin ƙasar, inda Hukumar Kula da Aukuwar Bala’i ta lardin ta ce mutum 307 sun mutu.

Kazalika an bayar da rahoton mutuwar mutum biyar a lardin Gilgit-Baltistan da mutum tara a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Pakistan, wanda ake kira Azad Jammu da Kashmir.

An fuskanci katsewar hanyoyin sadarwa a yankuna da dama sakamakon lalacewar turakun kamfanonin sadarwa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us