Kowane watan Agusta, bukukuwan tunawa da ranar samun 'yancin kai na India da Pakistan suna kira ga yin lissafi, damar yin tunani game da "alƙawarin" India ga Musulmai miliyan 35 waɗanda suka zaɓi zama a kasar a yayin rikicin raba kasar, lokacin da sabuwar jamhuriyar da ta bayyana yin adalci ga dukkan ‘yan kasa da rayuwarsu ta zamantakewa da al’adu.
A yanzu wannan al'ummar na da mutane miliyan 200, Musulmai ne kawai a Pakistan da Indonesia suka fi su yawa, kuma tana kan hanyar zama mafi yawan al'ummar Musulmi a duniya nan da 2060.
Amma duk da haka adadinsu kadai ba ya bayyana dalilin da ya kawo gargadin kungiyar Kasashen Musulmi a cikin shekarun 1940, cewa mulkin jam'iyyar "Hindu Congress" zai mayar da Musulmin Indiya saniyar ware a siyasance, tare da nuna musu wariya a zamantakewa da harkokin tattalin arziki, lalata al'adunsu, da jefa su a tashin hankali da gangan.
Dimokuradiyyar da babu ruwan ta da wani addini, samar da adalci a fannin doka ga dukkan 'yan kasa su ne tushen alƙawarin kafuwar India, wani mataki na ƙin yarda da ra'ayin 'yan kishin Hindu na raba kasa, inda aka dasa tushen ƙirƙirar ƙasar Musulmin Pakistan da kasar Hindu ta India, wanda akida ce ta 'Hindu Rashtra'.
Tabbas, har zuwa Disamban 2019, India mai aiki da dimokuradiyya ba ta da wata matsalar addini na Indiyanci.
An kawo karshen wannan ra’ayi da aka kafa kasar a kai ne tare da Kwaskwarima ga Dokar Zama Dan Kasa, wadda ta kawo ka’idojin duba addinin mutum don karbar sa a matsayin dan kasar.
Al’amuran da suka biyo baya, ciki har da harin ta'addanci da aka kai bayan Pahalgam na murkushe wadanda ake kira bakin haure ‘yan Bangladesh ba tare da izini ba, sun kara dagula wannan yanayin ne kawai, wanda ke nuna karuwar kudurin kasar na kakaba nuna wariya ta hanyar kallon wanne addini mutum ke bi.
A Gujarat, Maharashtra, New Delhi, da sauran wurare, 'yan sanda na kama Musulmai ‘yan Bengali - yawancin su matalauta da ke kwadago - suna bayyana su a matsayin masu zama "ba bisa doka ba" kuma, a lokuta da yawa, suna yin hakan ba tare da wani taƙaitaccen bayani a gaban alkali ba.
Dokar ta ba wa hukumomi damar ɓata Musulman India waɗanda ba su da shaidar tabbatar da zama 'yan ƙasar India na asali, barazana mummuna a ƙasar da ke da miliyoyin matalauta da marasa galihu da ba su da irin wannan takarda.
Sai da duk da haka, wadanda ba Musulmi ba, za su ci gaba da hakkin zama 'yan kasa a karkashin doka.
Tushen nuna wariya
Wannan sauyi ne mai karya zuciya da ya saba wa matakan da aka kafa kasar a kai. Ha'inci ne ga alkawarin da aka yi a bayyane - saba wa hali, shari'a, da tsarin mulki - ga Musulmin India.
Hakan ya mayar da rikice-rikicen zamantakewa da siyasa da na tarihi tsakanin Hindu masu rinjaye da mafi yawan 'yan tsiraru zuwa kayan aikin dabbaka manufofin kasa.
Rarraba jama'a ba zai iya sake jawo zargi daga jami'an zabe ko kotuna ba - jam’iyyar BJP a lokacin zaben majalisar dokokin jihar Jharkhand a 2024 ta yi alƙawarin ɗaukar matakin fatattakar 'yan Bangladesh ba bisa ƙa'ida ba'.
Duka su biyun sun zama musabbabin tsare Musulmi da ake yi a halin yanzu. Yawancin wadanda ake tsare da su suna da isassun hujjoji, an bayar da rahoto sosai kan batun, amma hakan bai hana hukumomi ci gaba da tsare su na kwanaki ba, ko kuma tilastawa a ‘kore su’ a iyakar jihar West Bengal — tsarin korar da ba ya bisa dokokin India ko na kasa da kasa kan hakkin bakin haure.
An shirya tantance takardun masu jefa kuri’a miliyan 80 inda za a goge sunayen bakin haure da dama daga jerin rajistar masu zaben kafin wtaan Nuwamban 2025. Za a yi hakan ne a jihar Bihar inda za a gudanar da kwaskwarima ga harkokin zabe.
Duk waɗannan matakan sun yi daidai da cin amanar wancan alkawari na ainihi ga Musulmai da aka kulla a 1947.
Wadanda suka kalli rabuwar da aka yi ba a matsayin hadin gwiwa wajen samar da kasar Musulunci da kasar Hindu ba, sai a matsayin wata mummunar tarwatsewar tarihin matsayin India mai al’ummu da yawa, yanzu za a tilasta musu sake tantance abubuwan da ke faruwa ta hanyar wani kundin bayani da Jinnah ya gabatar.
"Dunkulalliyar India na nufin bautar da Musulmai da mamaye su baki daya da Indiayawa suka yi a wannan karamar nahiyar," in ji Jinnah a cikin wata sanarwa a watan Disamban 1945, "kuma wannan shi ne abin da Majalisar Hindu ke neman cim ma wa a yau..."
Shaidar ba ta keɓanta ga matalautan ma'aikata Musulmi ba.
Masana’antar shirya fina-finai ta Bollywood, babbar mai yada al'adun India a kasashen waje kuma mai sauya tunanin jama’a, ta yi shiru a yayin da alkalai suka sanar da bayar da lambobin yabo na cinema na kasa guda biyu ga shirin fim din Kerala Story (2023), fim ɗin da aka shirya kan da'awar da ba ta dace ba game da matan Musulmi daga Kudancin jihar Kerala da aka yi safararsu don yin hidima ga ISIS.
A halin da ake ciki, sakamakon durkushewar kudi, masana'antar na ci gaba da bayar da siffofi na miyagu kamar yadda aka saba: 'yan ta'addar Musulunci, Sarkin Musulmi azzalumi, dillalin muggan kwayoyi mai suna Zubair.
A jihar Karnataka da ke kudancin kasar, an kama wasu shugabannin kungiyar Hindutva dangane da guba da aka duba a wani tankin ruwa na makarantar gwamnati, don kitsa tuggun ganin an cire shugaban makarantar tare da korar sa daga aiki.
Duk wanda ya yi amfani da ayyukan gig ya san ɓoyayyiyar tsanar da suke wa abokan cinikin su. Wata ƙwararriyar gyara gashi ta gaya mani cewa tana cikin fargaba game da ziyartar wasu rukunin gidaje a babban birnin kasuwanci, Mumbai, inda masu gadi da mazauna wurin suke bukatar ta cire niqaab din ta, bayanin da ya yi daidai da rubuce-rubuce da bayanan da aka samu daga direbobin taksi da abokan hulɗa.
Hasashen da aka gudanar ya bayyana cewa samu ma'aikata miliyan 23.5 nan da shekarar 2029-30, kuma a cikin waɗannan bayanan masu cike da son kai, sakon na bayyana ana gina tattalin arikin India tare da rufe kofofinsa ga miliyoyin ‘yan kasa. Ana tsara tattalin arzikin India a yau ta yadda yake barin wasu a baya.
Nuna tsana na yau da kullum
Waɗannan abubuwan da suka faru na nuna irin tashin hankali da ake fuskanta yau da kullun wajen nuna ƙiyayyar Indiyawa ga Musulmai.
Haramcin cin naman saniya; yawaitar kai hare-haren kisan gilla kan Musulmi masu sayar da nama da ake zargi da safara ko adana shi; nuna bambanci wajen rrusa gidaje da kadarori na Musulmi da ake zargi a rikicin kabilanci; dan karamin adadin Musulmai a Majalisar Dokoki da Majalisun Jihohi; da izgili da rera waƙoƙin gungun matasan Hindu a bakin Masallatai a lokacin bukukuwan Hindu—duk suna nuni ne ga ƙirƙirar ‘Akidar Indiyanci’ da ba ta da juriya ga duk wanda daga al’ummarta ya fito ba.
Tun a shekara 1952, taron yankin Urdu da Anjuman-Taraqqi-i-Urdu suka yi sun bayyana yadda aka soke Urdu a makarantun Firamare na jihar Uttar Pradesh.
Jawaharlal Nehru, a daya daga cikin wasiku kusan 400 da ya rubuta wa manyan ministoci a lokacin yana firaminista, ya nuna bacin ransa a kokarin da ake yi a jihar arewa na fitar da wani yare wanda “ya girmama a al’adu da tunanin India”.
A cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 16 ga Yuli 1953, Nehru ya ce Indiyawa suna yin watsi da gazawarsu, wanda sai a ce "zo ku mamaye mu".
"Akwai wani abu da ke wargajewa a yanayin zamantakewar mu," in ji shi, game da shagaltuwar da yake da ita don magance matsalolin zamantakewa. "Wataƙila wannan ya faru ne saboda tsawon shekaru da muka yi muna aiki a ƙarƙashin tsarin kabilanci, wanda ke raba mu zuwa bangarori daban-daban.
“Koma mene ne dai, a bayyane yake cewa muna son wargajewa kuma muna aiki a cikin ƙananan ƙungiyoyi da ke janyo kowace irin tsokana."
Bambance-bambance tsakanin 1953 da 2025 na iya zama matakan da gwamnati ke dauka game da rarrabuwar kawuna da kabilanci.
A wajen wani gangamin zabe a shekarar 2024, Firaminista Modi ya kira Musulmai a matsayin ''masu kutsa kai'', yana mai ikirarin cewa Majalisar Dokoki za ta nemi sanya Musulmai su zama masu cin gajiyar albarkatun kasa da ke kan gaba; kuma wai Majalisar Majalisun za ta kwace dukiyar mafi yawan mabiya addinin Hindu da suka sha wahala wajen tara wa, da suka hada da sarkokin mata ke da shi, a wani yunkuri na sake raba arzikin ga wadanda suka “da ‘ya’ya da yawa”.
Jam’iyyar BJP ta rasa kujerar yankin da aka gudanar da wannan gangami, sannan kuma cikin ban kunya ta rasa kujerar majalisa mai wakiltar Faizabad-Ayodhya inda Modi ya kaddamar da haikalin Ram watannin baya.
Masanin falsafa Hannah Arendt ya yi gargaɗin cewa ba tare da shiga cikin harkokin siyasa ba, 'yan ƙasa ba wai kawai muryarsu suke rasa wa ba, har ma da 'yancinsu.
Ga miliyoyin 'yan India, musamman Musulmai, wannan gargaɗin ba a baki kawai yake ba. Rushe wata hukuma, cire hannaye daga yanke wani hukunci, da mayar da su baki a cikin kasarsu, haƙƙoƙin da aka taba bayyana su da cewa ba za a iya hana duk wani dan India amfani da su ba, a yanzu ana sauya musu fasali, sannan ma sannu a hankali ana shafe su gaba daya.