Ukraine ta yi ikirarin cewa sojojinta sun jawo wa Koriya ta Arewa asarar dakaru fiye da 30 a yankin Kursk da ke kan iyakar Rasha, inda Kiev ta kaddamar da farmaki a cikin watan Agusta.
Sanarwar da Hukumar Leken Asiri ta kasar Ukraine (HUR) ta fitar ta kafar Telegram ta bayyana cewa, ko dai a kalla sojojin Koriya ta Arewa 30 ne sojojinta suka kashe ko kuma suka jikkata su a ranakun 14 da 15 ga watan Disamba a kusa da kauyukan Plechovo da Vorozhba, da Martynovka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, akalla ma'aikatan Koriya ta Arewa uku kuma sun bace a kusa da kauyen Kurilovka.
Ta kara da cewa saboda wannan asarar da aka samu, wasu dakarun na Koriya ta Arewa na ci gaba da daƙile kungiyoyin da ke kai farmaki a yankin.
Har yanzu dai hukumomin Rasha da na Koriya ta Arewa ba su ce uffan ba game da wannan ikirarin, kuma tabbatar da gaskiyar ikirarin na Ukraine na da wahala sakamakon yakin da ake yi.