Akwai yiwuwar ganawa tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a wani taro da za a gudanar a farkon mako mai zuwa, in ji fadar Kremlin a ranar Alhamis.
Ganawar za ta zama ta farko tsakanin Shugaban Amurka mai ci da na Rasha tun bayan da Joe Biden ya gana da Putin a Geneva a watan Yunin 2021, kuma zai zo ne a daidai lokacin da Trump ke kokarin kawo karshen hare-haren da Rasha ke kaiwa Ukraine.
“Bisa shawarar bangaren Amurka, an cim ma wata yarjejeniya kan manufa ta gudanar da taron ƙoli na kasashen biyu a cikin kwanaki masu zuwa,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Rasha ya nakalto Yuri Ushakov jami’i a Fadar Kremlin yana cewa.
"Yanzu mun fara aiwatar da bayanan tare da takwarorinmu na Amurka. An sanya mako mai zuwa a matsayin lokacin da aka yi niyya," a cewar Ushakov.
Ushakov ya kuma kara da cewa, “an amince da wurin da za a gudanar da taron,” amma bai yi karin bayani kan taƙamaiman inda za a gudanar da taron ba.
Sanarwar ta zo ne kwana guda bayan da wakilin Amurka Steve Witkoff ya gana da Putin a Moscow.
Witkoff ya ba da shawarar a hada ganawar da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, amma Rasha ba ta ba da amsa kan wannan shawara ba, in ji Ushakov.
Ya kuma kara da cewa "Bangaren Rasha sun bar wannan zabi a buɗe ba tare da yin tsokaci ba."