AFIRKA
2 minti karatu
Ghana ta rufe gidajen rediyo tara kan saɓa ƙa'idojin watsa labarai
Wannan matakin ya biyo bayan wa’adin afuwa na wata guda da shugaban ƙasa John Dramani Mahama ya bayar ga tashoshin da ba su cika ƙa’idoji ba domin gyara kurakuransu na karya dokokin yaɗa shirye-shirye a zangon FM.
Ghana ta rufe gidajen rediyo tara kan saɓa ƙa'idojin watsa labarai
Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani na Ghana Sam George ne ya sanar da rufe gidajen rediyon a shafinsa na Facebook. / Getty Images
14 Agusta 2025

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCA) a Ghana ta rufe tashoshin rediyo tara saboda gaza bin ƙa’idojin yaɗa shirye-shirye bayan kwanaki 30 na wa’adin sassauci da shugaban ƙasa ya bayar.

Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani na Ghana Sam George ne ya sanar da rufe gidajen rediyon a shafinsa na Facebook.

Wannan matakin ya biyo bayan wa’adin afuwa na wata guda da shugaban ƙasa John Dramani Mahama ya bayar domin bai wa tashoshin da ba su cika ƙa’idoji ba damar gyara kurakuransu na karya dokokin yaɗa shirye-shirye a zangon FM. Sai dai tashoshi shida ba su cika sharuɗɗan da hukumar ta bayar ba kafin ƙarewar wa’adin.

Wannan matakin ya shafi kafafen watsa labarai da dama a faɗin ƙasar waɗanda suka haɗa da:

  • Donplus Multimedia Limited (105.9 FM, Ho)

  • Dreams Ghana Media Limited (104.9 FM, New Abirem)

  • Jam Multimedia Limited (101.3 FM, Kintampo)

  • Jewel Group Limited (102.7 FM, Duayaw Nkwanta)

  • Kpandai Star Community Radio (107.3 FM, Kpandai)

  • Unique Gateway Communication Limited (105.7 FM, Nkawkaw)

Haka kuma, an dakatar da tashoshi uku mallakin Wontumi Multimedia Company Limited saboda aiki ba tare da Takardun Amincewa masu inganci ba. Tashoshin sun haɗa da 95.9 FM (Accra) da tashoshi biyu na 101.3 FM (Kumasi da Takoradi), bayan sun saɓa Sashe na 54 na dokokin Electronic Communications Regulations na shekarar 2011.

NCA ta bayyana cewa duk da cewa tashoshi da dama sun gyara kurakuransu a lokacin wa’adin sassaucin, waɗanda aka dakatar sun kasa magance manyan matsaloli kamar amfani da mitoci na watsa shirye-shirye ba bisa ƙa’ida ba da kuma amfani da wuraren watsa shirye-shirye da ba a amince da su ba.

Hukumar ta sake jaddada kudirinta na aiwatar da dokokin yaɗa shirye-shirye da tabbatar da cewa duk masu lasisin aiki sun bi ƙa’idojin hukuma. Wannan matakin ya nuna kokarin Ghana na kiyaye tsari a fannin rediyo tare da karfafa bin doka a fadin kasa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us