AFIRKA
2 minti karatu
Ƙungiyar RSF ta Sudan ta kashe fararen hula 18 a yammacin Khartoum
Ƙungiyar RSF wadda ke rikici da sojojin Sudan ta kashe mutanen ne a wani hari da dakarunta suka kai kan ƙauyuka biyu a yammacin Khartoum.
Ƙungiyar RSF ta Sudan ta kashe fararen hula 18 a yammacin Khartoum
Yaƙin Sudan wanda aka fara tun a 2023 ya yi sanadin mutuwar dubban mutane / Reuters
10 Agusta 2025

Ƙungiyar RSF ta Sudan ta kashe fararen hula 18 a wani hari da ta kai kan wasu ƙauyuka biyu da ke yammacin Khartoum a farkon makon nan, kamar yadda wata ƙungiya da ke sa ido ta tabbatar a ranar Asabar.

Dakarun ƙungiyar sun kai harin ne a ranar Alhamis a Jihar Kordofan ta Arewa, wanda yanki ne da ke da muhimmanci ga ƙungiyar ta RSF wurin fasa-ƙwaurin man fetur daga Libiya.

Yankin ya kasance babban fagen daga tsakanin sojoji da RSF tsawon watanni, kuma an katse duk wasu hanyoyi da jama’ar yankin za su sadu da sauran duniya waɗanda suka haɗa da wayoyi da intanet.
A cewar ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Emergency Lawyers, wacce ta riƙa rubuta laifukan da ake aikatawa tun farkon yakin da aka fara fiye da shekaru biyu da suka wuce, harin da aka kai ƙauyuka biyu a Kordofan ta Arewa ya kashe fararen hula 18 tare da jikkata ɗaruruwa.

An kai wadanda suka jikkata zuwa babban birnin jihar, El-Obeid, domin samun magani.

Yana da matukar wahala a tabbatar da adadin waɗanda abin ya rutsa da su a Sudan, saboda yawancin cibiyoyin kiwon lafiya sun daina aiki kuma kafafen yaɗa labarai suna da iyaka wajen samun labarai.

Tun bayan da RSF ta rasa iko da babban birnin kasar Khartoum ga sojoji a watan Maris, ta mayar da hare-harenta a yammacin ƙasar, inda take rike da yawancin yankin Darfur wanda ke da matuƙar girma.

Rikicin na Sudan ya kashe dubban ɗaruruwan mutane kuma ya haifar da abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a matsayin matsalar hijira da yunwa mafi girma a duniya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us